Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Bigire - Tana nufin guri ko gurbi.
Misali; Idan mutum yana sallah ana so ya kalli bigiren sujjadar sa.
ENG; Place (A turance tana nufin bigire)
Biki - Tana nufin tara mutane su ci su sha saboda taya murnar wani abin farin ciki da ya samu.
Misali; Zan je biki gobe da yamma, ƙanwata ce za ta yi aure.
ENG; Celebration (A turance tana nufin biki)
Biko - Tana nufin neman dawo da matar da ta yi yaji (wadda ta yi fushi ta bar gidan mijinta).
Misali; Kawu ya tafi bikon matar yaya Ado.
ENG; Attempt to reconcile run-away wife (A turance yana nufin biko)
Bilimbituwa - Tana nufin neman abu a rasa a yi ta bulayi, ko kuma neman da babu sakamako.
Misali; Mafarautan bilimbituwa kawai za su yi a dajin saboda babu namun daji yanzu.
ENG; Fruitless search (A turance tana nufin bilimbituwa)
Bincike - Tana nufin ƙoƙarin gano wani abu.
Misali; 'Yan sanda na bincike don gano masu aikata laifi.
ENG; Investigation (A turance yana nufin bincike)
Bindiga - Tana nufin na'aurar harbi musamman ga mayaƙa ko maharba ko jami'an tsaro.
Misali; Sojoji sun kama wani matafiyi da bindiga a hanyar Sokoto.
ENG; Gun (A turance tana nufin bindiga)
Bini-Bini - Tana nufin akai-akai.
Misali; Abokina bini-bini ya zo gidanmu, hakan ya sa mun shaƙu.
ENG; Repeatedly (A turance tana nufin bini-bini)
Binne - Tana nufin a haƙa rami a sa abu a rufe.
Misali; An binne mamacin a maƙabartar cikin gari.
ENG; Bury (A turance tana nufin binne)
Birgima - Tana nufin a yi ta juyi a ƙasa.
Misali; Yaron yana ta birgima don an hana shi fita wasa.
ENG; Rolling on the ground (A turance yana nufin birgima)
Biri - Tana nufin dabba mai yanayin siffar mutum.
Misali; Da muka je gidan ajiye namun daji mun ga biri da kura.
ENG; Monkey (A turance tana nufin biri)