Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Bini-Bini - Tana nufin akai-akai. Misali; Abokina bini-bini ya zo gidanmu, hakan ya sa mun shaƙu. ENG; Repeatedly (A turance tana  nufin bini-bini)
Binne - Tana nufin a haƙa rami a sa abu a rufe. Misali; An binne mamacin a maƙabartar cikin gari. ENG; Bury (A turance tana nufin binne)
Birgima - Tana nufin a yi ta juyi a ƙasa. Misali; Yaron yana ta birgima don an hana shi fita wasa. ENG; Rolling on the ground (A turance yana nufin birgima)
Biri - Tana nufin dabba mai yanayin siffar mutum. Misali; Da muka je gidan ajiye namun daji mun ga biri da kura. ENG; Monkey (A turance tana nufin biri)
Biris - Tana nufin nuna halin ko-in-kula da abu ko yin watsi da shi. Misali; Duk da yana cikin mawuyacin hali amma matarsa ta yi biris da shi saboda rashin kirkinsa. ENG; Ignore (A turance tana nufin biris)
Birjik - Tana nufin da yawa ko adadi mai yawa. Misali; Kaya ne birjik a shagon su Bala, sai wanda ka zaɓa. ENG; Abundantly (A turance tana nufin birjik)  
Birki - Tana nufin abin da ake takawa ko matsawa abin hawa ya tsaya, kamar keke ko mota ko babur da sauransu. Misali; Direban ya taka birki lokacin da shanu suka zo tsallaka titin. ENG; Brake (A turance tana nufin birki)
Birkice - Tana nufin a juya abu daga sama zuwa ƙasa. Misali; Ya birkice ɗakin yana neman maɓallin rigarsa. ENG; Overturn/upside down (A turance tana nufin birkice)
Birni - Tana nufin maraya ko inda ababben more rayuwa na zamani suke. Misali; A birni ake samun manyan gidaje da manyan makarantu Kishiyarta; Ƙauye ENG; Town (A turance tana nufin birni)
Bisa - Tana nufin a kan wani abu. Misali; Littattafan na bisa teburi. Kishiyarta; Ƙarƙashin ENG; On top/above (A turance tana nufin bisa)
1 28 29 30 31 32 298