Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Be eager -

A turance tana nufin ƙagauta.

Misali: Yaron ya ƙagauta ya je makaranta yau.

HAU; Ƙagauta (Tana nufin jin gaggawa ko tsananin son yin wani abu)

Be kind -

A turance tana nufin kyauta.

Misali: Ya kamata mu riƙa kyautata wa juna.

HAU; (Tana nufin nuna alheri, tausayi ko kyautatawa ga wasu)

Be on good terms with someone - A turance tana nufin jitu. Misali; Sun jitu da juna shi yasa ba sa faɗa. HAU; Jitu (Tana nufin shaƙuwa ko fahimtar juna)
Be Replete - A turance tana nufin koshi. Misali: Ya ƙoshi sosai bayan ya ci tuwo da miya. HAU: Ƙoshi (Tana nufin cikar ciki bayan cin abinci sosai)
Bean Cakes - A turance tana nufin ƙosai. Misali: Ta yi ƙosai da safe domin karin kumallo. HAU: Ƙosai (Tana nufin abincin da ake yi da markaɗaɗɗen waken da aka soya a mai)
Beard - A turance tana nufin gemu. Misali; Ya aske gemunsa ranar Lahadi. HAU; Gemu (Tana nufin gashin da yake fitowa a haɓar maza)
Beat - A turance tana nufin bugu. Misali; Ɓarayin sun sha bugu a hannun 'yansanda. HAU; Bugu (Tana nufin duka)
Beautification/Make-up - A turance tana nufin kwalliya. Misali: 'Yan matan sun yi kwalliya za su gidan biki. ENG; Kwalliya (Tana nufin yin ado ko ƙawatawa ta hanyar sanya kayan ado)
Beautiful - A turance tana nufin kyakkyawa. Misali: Aisha kyakkyawa ce sosai. HAU; Kyakkyawa (Tana nufin abu ko mutum mai kyau, mai jan hankali ko mai kyau a ido)
Become difficult to control - A turance tana nufin kangara. Misali; Shagwaɓa yara na sa su a halin kangara. HAU; Kangara (Tana nufin fitina ko gagara ko rashin ji)
1 26 27 28 29 30 337