Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Be on good terms with someone - A turance tana nufin jitu. Misali; Sun jitu da juna shi yasa ba sa faɗa. HAU; Jitu (Tana nufin shaƙuwa ko fahimtar juna)
Beard - A turance tana nufin gemu. Misali; Ya aske gemunsa ranar Lahadi. HAU; Gemu (Tana nufin gashin da yake fitowa a haɓar maza)
Beat - A turance tana nufin bugu. Misali; Ɓarayin sun sha bugu a hannun 'yansanda. HAU; Bugu (Tana nufin duka)
Become difficult to control - A turance tana nufin kangara. Misali; Shagwaɓa yara na sa su a halin kangara. HAU; Kangara (Tana nufin fitina ko gagara ko rashin ji)
Become Great - A turance tana nufin gawurta. Misali; Kamfanin sun gawurta, yanzu sukan fitar da kayayyakinsu zuwa ƙasashen ƙetare. HAU; Gawurta (Tana nufin shahara ko bunƙasa ko kai wa ƙololuwar matsayi)
Become Suddenly Angry - A turance tana nufin harzuƙa. Misali; Ya harzuƙa da yawa shi yasa ya kai masa naushi. HAU; Harzuƙa (Tana nufin saurin fushi)
Bed - A turance tana nufin gado. Misali; Ya siyo gado saboda bikin 'yarsa. HAU; Gado (Tana nufin abin da ake kwanciya a kai a yi bacci ko a huta)
Bed Bugs - A turance tana nufin kuɗin cizo. Misali; Ɗakin Musa akwai kuɗin cizo da yawa, idan ka shiga sai ka kwaso. HAU; Kuɗin Cizo (Tana nufin wani ƙwaro mai shan jini)
Bees-wax - A turance tana nufin kaki. Misali; Zumar mai kyau ce don a cikin kaki take. HAU; Kaki (Tana nufin saƙar zuma)
Begging - A turance tana nufin bara. Misali; Masu bara sun yawaita a duniya yanzu. HAU; Bara (Tana nufin roƙo ko bin mutane kana tambayar su baka abin hannunsu)
1 25 26 27 28 29 298