Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Biris - Tana nufin nuna halin ko-in-kula da abu ko yin watsi da shi. Misali; Duk da yana cikin mawuyacin hali amma matarsa ta yi biris da shi saboda rashin kirkinsa. ENG; Ignore (A turance tana nufin biris)
Birjik - Tana nufin da yawa ko adadi mai yawa. Misali; Kaya ne birjik a shagon su Bala, sai wanda ka zaɓa. ENG; Abundantly (A turance tana nufin birjik)  
Birki - Tana nufin abin da ake takawa ko matsawa abin hawa ya tsaya, kamar keke ko mota ko babur da sauransu. Misali; Direban ya taka birki lokacin da shanu suka zo tsallaka titin. ENG; Brake (A turance tana nufin birki)
Birkice - Tana nufin a juya abu daga sama zuwa ƙasa. Misali; Ya birkice ɗakin yana neman maɓallin rigarsa. ENG; Overturn/upside down (A turance tana nufin birkice)
Birni - Tana nufin maraya ko inda ababben more rayuwa na zamani suke. Misali; A birni ake samun manyan gidaje da manyan makarantu Kishiyarta; Ƙauye ENG; Town (A turance tana nufin birni)
Bisa - Tana nufin a kan wani abu. Misali; Littattafan na bisa teburi. Kishiyarta; Ƙarƙashin ENG; On top/above (A turance tana nufin bisa)
Bisani - Tana nufin daga baya ko kuma bayan. Misali; An ɗauke min kuɗina amma daga bisani an dawo min da su. ENG; Later (A turance tana nufin bisani)
Biscuit - A turance yana nufin biskit. Misali; Biskit ɗin kamfanin NASCO yana da daɗi da inganci. HAU; Biskit (Tana nufin abin ci na maramari da ake yi da fulawa da sikari da wasu sinadaran)
Bishara - Tana nufi labari mai daɗi. Misali; Malamin ya yi wa ɗalibai bishara da cinye jarabawarsu. ENG; Good news (A turance tana nufin bishara)
Bishiya - Tana nufin ice ko tsiro da yake fitowa haka kawai ko idan an shuka, yana da ganyayyaki da itatuwa a wasu lokutan. Misali; Idan an shuka bishiya takan ɗauki lokaci mai tsawo kafin ta girma. ENG; Tree (A turance tana nufin bishiya)
1 31 32 33 34 35 337