Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Bulo - Tana nufin abin da ake amfani da shi don yin gini. Misali; Gidan da aka gina da bulon siminti ya fi ƙarko. ENG; Cement Block (A turance tana nufin bulo)
Bulus - Tana nufin samun abu a arha ba tare da an sha wahala ba. Misali; Ya siyi gidan a bulus saboda mai gidan kuɗi yake buƙata. ENG;Something gotten cheaply (A turance tana nufin bulus)
Bundle of Grain - A turance tana nufin dami. Misali; Kaka ya ba mu dami guda na gero ɗazu. HAU; Dami (Tana nufin ƙunshi ko ɗaurin hatsi)
Bunsuru - Tana nufin namijin akuya. Misali; Malam Rabi'u ya siyo bunsuru shekaran jiya. Kishiyarta; Akuya ENG; He-goat (A turance tana nufin bunsuru)
Bunƙasa - Tana nufin samun gagarimin cigaba. Misali; Kantin ya bunƙasa yanzu suna shigo da kaya daga ƙasashen ƙetare. ENG; Develop into fullness (A turance tana nufin bunƙasa)
Burbuɗi - Tana nufin abin da ya marmashe ya zama gari. Misali; Ta yi amfani da burbuɗin biredi wajen suyar dankalin. ENG; Crumbs (A turance tana nufin burbuɗi)
Bureau of public Enterprises (BPE) - Hukumar Gwanjon kadarorin Gwamnati
Bureau of Public Enterprises (BPE) - Hukumar Gwanjon kadarorin Gwamnati
Bureau of Public Enterprises (BPE) - Hukumar gwanjon  kadarorin gwamnati
Bureau of Public Enterprises (BPE) - Hukumar gwanjon kadarorin gwamnti
1 35 36 37 38 39 298