Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Ƙaryata - Tana nufin ƙin amincewa da wani abu ko musanta shi. Misali: An zarge shi da laifi amma ya ƙaryata hakan. ENG: Deny (A turance tana nufin ƙaryata).
Ƙarzuwa - Tana nufin cutar fata da ƙazanta ke haifarwa, inda ƙananan ƙuraje ke fitowa a sassan jiki. Misali: Ƙarzuwa na iya yaɗuwa cikin sauri idan ba a kula da tsafta ba. ENG: Scabies (A turance tana nufin ƙurajen fata masu ƙaiƙayi)
Ƙarƙashi - Tana nufin abin da yake ƙasa. Misali: Katin ya faɗi a ƙarƙashin tebur. ENG: Underneath (A turance tana nufin ƙarƙashi).
Ƙasa - Tana nufin duniyar da muke rayuwa a kanta. Misali: Allah ya yi halittu masu yawa a doron ƙasa. ENG: Earth (A turance tana nufin ƙasa).
Ƙasa-ƙasa -

Tana nufin launi, kamar ruwan ƙasa mai duhu.

Misali; Ƙasan gonar ya yi ƙasa-ƙasa bayan ruwan sama ya sauka.

ENG; Brownish (A turance tana nufin ƙasa-ƙasa)

Ƙasaita -

Tana nufin isa ko zama gawurtacce ko mai muhimmanci ko tasiri a wani fanni.

Misali: Bayan shekaru, ya ƙasaita a fagen siyasa saboda ƙwarewarsa.

ENG: Become important / influential (A turance tana nufin ƙasaita)

Ƙasan -

Tana nufin ɓangaren ƙasa na wani abu.

Misali: Ƙasan dutsen akwai kogin da ke gudana.

ENG: At the bottom of (A turance tana nufin ƙasan)

Ƙashi -

Tana nufin wani ɓangare na jikin dabbobi ko mutum wanda ke ba da tsari da ƙarfi ga jiki.

Misali: Likitan ya gano cewa yaron ya karye a ƙashin hannunsa.

ENG: Bone (A turance tana nufin ƙashi)

Ƙato -

Tana nufin girma sosai.

Misali: Gidan sabon sarki ƙato ne sosai kowa na mamakin girmansa.

ENG: Huge (A turance tana nufin ƙato)

Ƙauna -

Tana nufin jin soyayya.

Misali; Uwa tana nuna ƙauna ga ɗanta ta hanyar kulawa da shi da kyau.

ENG; Affection (A turance tana nufin ƙauna)

1 324 325 326 327 328 330