Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Ƙarfe - Tana nufin wani irin abu mai ƙarfi da ake amfani da shi wajen ƙera kayayyaki kamar ƙofa, mota, ko cokali da sauransu. Misali: Ma’aikacin ya sa ƙofar ƙarfe a shagon. ENG: Metal (A turance tana nufin ƙarfe)
Ƙarfi - Tana nufin kuzarin da mutum yake da shi ko ikon aikata aiki. Misali: Ma'aikatan na buƙatar ƙarfi domin ɗaga kaya masu nauyi.. ENG: Strength (A turance tana nufin ƙarfi).
Ƙari - Tana nufin ƙara wani abu fiye da yadda yake a da. Misali: Farashin kaya ya ƙaru a wannan watan. ENG: Increase (A turance tana nufin ƙari ko ƙaruwa).
Ƙari - Tana nufin dafin  ƙudan zuma, maciji ko kunama da ke jawo zugi ko kumburi. Misali: An cire masa ƙari bayan kunama ta harbe shi. ENG: Sting of bee (A turance tana nufin ƙari).
Ƙarko - Tana nufin ƙarfin ko juriya ko daɗewa. Misali: Wannan kujera tana da ƙarko sosai saboda an yi ta da katako mai kyau. ENG: Durability (A turance tana nufin ƙarko).
Ƙarni - Tana nufin shekaru ɗari. Misali: Wannan gini ya wanzu tun ƙarni da ya gabata. ENG: Century (A turance tana nufin ƙarni).
Ƙaro - Tana nufin wani abu mai ɗanko da ke fitowa  a jikin bishiya. Misali: Ana amfani da ƙaro wajen yin tawadar da ake rubutu. ENG: Gum (A turance tana nufin ƙaro).
Ƙarshe - Tana nufin kankat wato daga nan ba ƙari ko cigaba. Misali: Fim ɗin da muke gani ya zo ƙarshe. ENG: End (A turance tana nufin ƙarshe).
Ƙaru - Tana nufin ƙaruwa ko ƙara yawa. Misali: Yawan ɗalibai ya ƙaru a makarantar wannan shekara. ENG: Increase (A turance tana nufin ƙaru).
Ƙarya - Tana nufin faɗin magana wadda ba gaskiya ba. Misali: Ya faɗi ƙarya domin ya gujewa hukunci. ENG: Lie (A turance tana nufin ƙarya).
1 323 324 325 326 327 330