Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ƙandare - Tana nufin bushewa ko zama babu ruwa.
Misali; Rijiyar ta ƙandare saboda tsananin zafi.
ENG; Become dry (A turance tana nufin ƙandare)
Ƙandas - Tana nufin abu mara maiƙo ko wanda man sa ya ƙare.
Misali; Miyar nan ta yi ƙandas saboda babu mai sosai a ciki.
ENG; Lacking oil (A turance tana nufin ƙandas)
Ƙani - Tana nufin ɗan’uwa namiji wanda yake bin wasu ma'ana yayye.
Misali; Ƙanina yana makaranta tare da abokansa.
ENG; Younger brother (A turance tana nufin ƙani)
Ƙanjame - Tana nufin ramewa ko sirancewa.
Misali; Ya ƙanjame sosai bayan doguwar jinyar da ya yi.
ENG; Become thin (A turance tana nufin ƙanjame)
Ƙanwa - Tana nufin ‘yar’uwa mace wadda take da yayye.
Misali; Ƙanwata tana makarantar firamare.
ENG; Younger sister (A turance tana nufin ƙanwa.)
Ƙanzo - Tana nufin ragowar abincin da ke maƙalewa a cikin tukunya idan an gama girki.
Misali; Idan an gama tuwo, za mu kwashi ƙanzo don mu shanya.
ENG; Scraps of food stuck to the pot (A turance tana nufin ƙanzo)
Ƙanƙamo - Tana nufin mutum mai rowa, wanda baya son yin kyauta.
Misali; Wannan mutumin ƙanƙamo ne, baya son taimakon kowa da kuɗinsa.
ENG; Stingy (A turance tana nufin ƙanƙamo.)
Ƙanƙance - Tana nufin raguwa ko komawa ƙarami.
Misali; Idonsa ya ƙanƙance saboda ciwon da yake yi.
ENG; Become small (A turance tana nufin ƙanƙance.)
Ƙanƙani - Tana nufin abu ƙarami ko mara girma.
Misali; Na sayi ƙanƙanin littafi domin yara su riƙa karantawa.
ENG; Small (A turance tana nufin ƙanƙani.)
Ƙanƙara - Tana nufin ruwa da ya daskare sakamakon tsananin sanyi.
Misali; A lokacin sanyi, ana iya ganin ƙanƙara a saman ruwa.
ENG; Ice (A turance tana nufin ƙanƙara)