Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ƙara - Tana nufin maimaita wani abu ko yin sa sau biyu ko fiye.
Misali; Malam ya ce a ƙara karanta darasin domin a fahimce shi sosai.
ENG; Repeat (A turance tana nufin ƙara)
Ƙaraji - Tana nufin ihu ko kuka mai ƙarfi saboda ciwo ko wahala.
Misali; Yaron ya yi ƙaraji lokacin da ya faɗi ya ji rauni.
ENG; Crying out in pain (A turance tana nufin ƙaraji)
Ƙarambau - Tana nufin cutar fata da ke sa ƙuraje ƙanana masu ruwa su fito a jiki, musamman ga yara.
Misali; Yaron ya kamu da ƙarambau, don haka ba ya zuwa makaranta har sai ya warke.
ENG; Chickenpox (A turance tana nufin ƙarambau)
Ƙaranci - Tana nufin rashin isa ko rashin wadata ko rashin kai wa wani adadi.
Misali; Akwai ƙarancin abinci a kasuwa saboda ana fama da fari.
ENG; Shortage (A turance tana nufin ƙaranci)
Ƙarangiya - Tana nufin wata irin ciyawa mai ƙaya da ke manne wa tufafi ko fata.
Misali; Yara sun guji shiga cikin ƙarangiya saboda suna tsoron kar ta manne musu.
ENG; Grass with prickly burrs (A turance tana nufin ƙarangiya.)
Ƙararrawa -
Tana nufin wani abu na ƙarfe da ake bugawa mai ƙara, wanda ake amfani da shi wajen sanarwa ko faɗakarwa.
Misali; An buga ƙararrawa domin ɗalibai su shiga aji.
ENG; Bell (A turance tana nufin ƙararrawa)
Ƙarasa -
Tana nufin kammala wani abu ko kaiwa ƙarshe.
Misali; Na ƙarasa aikin gida kafin dare ya yi.
ENG; Finish (A turance tana nufin ƙarasa)
Ƙare - Tana nufin kammala wani abu gaba ɗaya ko gamawa da shi.
Misali; Ta ƙare karatun littafin cikin kwana biyu.
ENG; Complete (A turance tana nufin ƙare)
Ƙarfafa - Tana nufin maganganun da ke ba da ƙwarin gwuiwa ga wanda ake yi wa su.
Misali; Malamin yana ƙarfafa wa ɗalibai gwiwa don su riƙa yin karatu sosai.
ENG; Strengthen (A turance tana nufin ƙarfafa)
Ƙarfamfana - Tana nufin datti ko ƙura da ke taruwa a cikin aljihu.
Misali: Ya wanke ƙarfamfana da ke cikin aljihunsa kafin ya sa rigar.
ENG: Dirt inside pocket (A turance tana nufin ƙarfamfana)