Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Tana nufin jiki ko wani sashen jiki ya yi tauri ko ya daskare na ɗan lokaci, yawanci saboda tsoro, sanyi ko jin zafi.
Misali; Wuyansa ya ƙage bayan ya yi tsalle ya faɗo daga sama.
ENG: Become temporarily stiff (A turance tana nufin ƙage).
Tana nufin zargin mutum da wani abu da be aikata ba ko ba tare da hujja ba.
Misali: An yi masa ƙagen ya saci kuɗi.
ENG: False accusation (A turance tana nufin ƙage)
Tana nufin wani abu mai ƙarfi da ke fitowa a kan dabba kamar shanu, awaki ko tumaki.
Misali: Shanu suna da ƙaho a kansu.
ENG: Horn (A turance tana nufin ƙaho)
Tana nufin wani abu mai kaifi da ke fitowa a ƙafar dabba (musamman zakara ko wasu tsuntsaye) da suke amfani da shi wajen kare kai ko faɗa.
Misali; Zakara yana amfani da ƙaiminsa wajen faɗa.
ENG; Spur (A turance tana nufin ƙaimi)
Tana nufin jin son sosa wani guri ko sashen jiki.
Misali: Yana jin ƙaiƙayi a hannunsa bayan sauro ya cije shi.
ENG: Itching (A turance tana nufin ƙaiƙayi)