Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Tana nufin barin wani wuri zuwa wani wuri.
Misali; Iyalan sun yi ƙaura daga ƙauyensu zuwa birni domin samun ayyukan yi.
ENG; Move to another place (A turance tana nufin ƙaura)
Tana nufin jar dawa.
Misali: Ɗahiru ya shuka ƙaura a gonarsa wannan kakar.
ENG: Red Guinea-corn (A turance tana nufin ƙaura)
Tana nufin daina zuwa wani wuri ko daina ziyartar wani.
Misali; Tun bayan rikicin da aka yi, mutane da dama sun yi ƙaurace wa zuwa kasuwar ƙauyen.
ENG; Stop visiting a place (A turance tana nufin ƙaurace)
Tana nufin warin abincin da ya ƙone ko wani abu da ya ƙone.
Misali: Ƙaurin abinci nake ji, da alama kin cikawa girkin wuta.
ENG: Smell of burnt food or something (A turance tana nufin ƙauri)
Tana nufin karkara ko inda ba birni ba.
Misali: Habu ya tafi ziyara ƙauyen kakansa a ƙarshen mako.
ENG: Village (A turance tana nufin ƙauye)
Tana nufin macen da ake da alaƙar abota da ita.
Misali: Fatima ta tafi kasuwa tare da ƙawarta.
ENG: Female friend (A turance tana nufin ƙawa)
Tana nufin son mallakar abu fiye da kima ko buƙata, musamman dukiya ko abinci.
Misali: Ƙawa-zucin ɗan kasuwar ya sa ya ci gaba da tara dukiya ba tare da taimakon wasu ba.
ENG: Greed (A turance tana nufin ƙawa-zuci)
Tana nufin zobe.
Misali: Mata na sanya ƙawanya a yatsunsu a matsayin kayan ado.
ENG: Any metal ring (A turance tana nufin ƙawanya)
Tana nufin gyara wani abu don ya zama mai kyau ko abin kallo.
Misali: Ta ƙawata ɗakin bikin ta da furanni da fitilu masu launi.
ENG: Make beautiful (A turance tana nufin ƙawata)