Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ƙaye - Tana nufin iya kwalliya ko tsara sutura domin jan hankali ko burgewa.
Misali: Matashin ya yi shiga mai ban ƙaye a wajen bikin da sabbin kaya masu kyau.
ENG: Showing off one’s stylishness of dress (A turance tana nufin ƙaye)
Ƙayyade - Tana nufin sanya doka, sharaɗi, ko iyaka, ko cimma yarjejeniya.
Misali: Sun ƙayyade dokokin da za a bi wajen gudanar da taron.
ENG: Rule / Agreement (A turance tana nufin ƙayyade)
Ƙazami - Tana nufin Mutum mara tsafta. Ana amfani da ita wajen bayyana mutum, wuri, ko kaya da ba su da tsabta.
Misali: Rigarsa ta zama ƙazami bayan ya yi aiki a gona.
ENG: Dirty (A turance tana nufin ƙazami)
Ƙazanta - Tana nufin yanayin datti ko rashin tsafta na jiki, muhalli, ko wani abu.
Misali: Ƙazanta a muhalli na iya jawo cututtuka kala-kala.
ENG: Dirtiness (A turance tana nufin ƙazanta)
Ƙaƙale -
Tana nufin mutum ya zama mai tsananin tsantseni ko zaɓi fiye da kima, har yana wahalar da kansa ko wasu wajen yin komai.
Misali; Yana ƙaƙale sosai wajen zaɓen abinci.
ENG; Being over-fastidious (A turance tana nufin ƙaƙale)
Ƙaƙƙautawa -
Tana nufin yin abu ba tare da tsayawa ba.
Misali; Ruwan sama yana zuba ba ƙaƙƙautawa tun safe har yamma.
ENG; Non stop (A turance tana nufin ƙaƙƙautawa)
Ƙa’ida -
Tana nufin dokoki ko tsarin da aka kafa domin tafiyar da al’amura cikin tsari.
Misali: Ma'aikatan suna aikinsu bisa ƙa'ida.
ENG: Regulation (A turance tana nufin ƙa’ida)
Ƙera - Tana nufin aikin sarrafa ƙarfe ko ƙirƙirar kayan aiki ta hanyar amfani da wuta da guduma.
Misali: Maƙeri yana ƙera fartanya, wuƙa, da sauran kayayyakin noma.
ENG: Forge (A turance tana nufin ƙera)
Ƙerere - Tana nufin tsayuwa ba tare da ladabi ko girmamawa ba.
Misali: Yaron ya tsaya ƙerere a gaban manya ba tare da nuna ladabi ba.
ENG: Stood disrespectfully (A turance tana nufin ƙerere)
Ƙeta - Tana nufin aikata wani mummunan abu da nufin cutarwa ko yin sharri ga wani.
Misali: Ƙeta ce raba makaho da sandarsa.
ENG: Malicious Act (A turance tana nufin Ƙeta)