Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Ƙirgi -

Tana nufin sarrafaffiyar fatar saniya, da ake amfani da ita wajen yin takalma, jaka, ko sauran kayayyaki.

Misali: Akan yi amfani da ƙirgi wajen yin takalma masu ƙwari.

ENG: Tanned cowhide (A turance tana nufin ƙirgi)

Ƙiri - Tana nufin buɗe ido sosai saboda mamaki, tsoro, ko kulawa. Misali: Musa ya yi ƙiri da ido lokacin da ya ga abin mamaki. ENG: Being wide eyed (A turance tana nufin ƙiri)
Ƙirin - Tana nufin ƙarfafa ko bayyana baƙin launi sosai. Misali: Hadari ya haɗo, gari ya yi baƙi ƙirin. ENG: Emphasizes blackness (A turance tana nufin ƙirin).
Ƙiriniya - Tana nufin wasa ko ɗabi’ar yin shirme da rashin ji irin na ƙananan yara. Misali: Ƙiriniyar yara a cikin gida tana sa iyaye yawan yin magana. ENG: Playful mischievousness especially by children (A turance tana nufin ƙiriniya)
Ƙiris -

Tana nufin kaɗan.

Misali: Saura ƙiris a fara shirin da nake son na kalla a talabijin.

ENG: A little bit (A turance tana nufin ƙiris)

Ƙirji -

Tana nufin sashen jikin mutum da ke tsakanin wuya da ciki.

Misali: Ya ji ciwo a ƙirji bayan ya yi gudu mai tsawo.

ENG: Chest (A turance tana nufin ƙirji)

Ƙiƙam - Tana nufin tsayawa ƙyam a gaban wani. Misali: Yaron ya ƙiƙam a gaban malaminsa yana sauraron darasi. ENG: Stood in front (A turance tana nufin tsayawa a gaba).
Ƙufula - Tana nufin saurin fushi. Misali; Ƙufula ya yi har ta kai ga ya mare shi. ENG; Quick-Tempered (A turance tana nufin ƙufula)
Ƙwadago - Dukkan wani irin aikin da mutum zai yi a biya shi kudi a matsayin lada ko albashi.
Ƙwaƙƙwafi - Bin diddigi domin gano wani ɓoyayyen al'amari.
1 328 329 330