Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ƙiyasi - Tana nufin kwatanta abu da wani abu domin bayyana kamanceceniya ko fahimtar ma’ana.
Misali: Malamin ya yi ƙiyasi tsakanin zuciya da injin mota wajen bayyana yadda suke aiki.
ENG: Analogy / Comparison (A turance tana nufin ƙiyasi)
Ƙiyasta - Tana nufin aunawa ko tantance abu ta hanyar tunani ko hasashe domin sanin ƙimarsa ko yadda yake.
Misali: Alƙalin ya ƙiyasta ra’ayoyin ɓangarorin biyu kafin ya yanke hukunci.
ENG: Estimate / Weigh / Consider (A turance tana nufin ƙiyasta)
Ƙiyayya - Tana nufin tsananin rashin so ko gaba tsakanin mutane ko ɓangarori guda biyu.
Misali: Ƙiyayya tsakanin maƙwabta na iya hana zaman lafiya a unguwa.
ENG: Hatred / Mutual Hatred (A turance tana nufin ƙiyayya)
Ƙiƙam - Tana nufin tsayawa ƙyam a gaban wani.
Misali: Yaron ya ƙiƙam a gaban malaminsa yana sauraron darasi.
ENG: Stood in front (A turance tana nufin tsayawa a gaba).
Ƙoda - Tana nufin wata muhimmiyar gaɓa da ke cikin ciki wadda ke tace jini tare da fitar da datti ta fitsari.
Misali: Likita ya ce alamomin lalurarsa na kama da na ciwon ƙoda.
ENG: Kidney (A turance tana nufin ƙoda)
Ƙodago - Tana nufin yin aiki domin samun kuɗi ko lada.
Misali: Ya fita ƙodago domin ya sami abin tallafa wa iyalinsa.
ENG: Labour / Any Work for Wages (A turance tana nufin ƙodago)
Ƙofa - Tana nufin hanyar shiga ko fita ta ɗaki, gida ko wani wuri.
Misali: Ya tsaya a bakin ƙofa yana jiran a buɗe masa.
ENG: Door / Doorway (A turance tana nufin ƙofa)
Ƙufula - Tana nufin saurin fushi.
Misali; Ƙufula ya yi har ta kai ga ya mare shi.
ENG; Quick-Tempered (A turance tana nufin ƙufula)
Ƙwadago - Dukkan wani irin aikin da mutum zai yi a biya shi kudi a matsayin lada ko albashi.
Ƙwaƙƙwafi - Bin diddigi domin gano wani ɓoyayyen al'amari.