Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Ƙirgi -

Tana nufin sarrafaffiyar fatar saniya, da ake amfani da ita wajen yin takalma, jaka, ko sauran kayayyaki.

Misali: Akan yi amfani da ƙirgi wajen yin takalma masu ƙwari.

ENG: Tanned cowhide (A turance tana nufin ƙirgi)

Ƙiri - Tana nufin buɗe ido sosai saboda mamaki, tsoro, ko kulawa. Misali: Musa ya yi ƙiri da ido lokacin da ya ga abin mamaki. ENG: Being wide eyed (A turance tana nufin ƙiri)
Ƙirin - Tana nufin ƙarfafa ko bayyana baƙin launi sosai. Misali: Hadari ya haɗo, gari ya yi baƙi ƙirin. ENG: Emphasizes blackness (A turance tana nufin ƙirin).
Ƙiriniya - Tana nufin wasa ko ɗabi’ar yin shirme da rashin ji irin na ƙananan yara. Misali: Ƙiriniyar yara a cikin gida tana sa iyaye yawan yin magana. ENG: Playful mischievousness especially by children (A turance tana nufin ƙiriniya)
Ƙiris -

Tana nufin kaɗan.

Misali: Saura ƙiris a fara shirin da nake son na kalla a talabijin.

ENG: A little bit (A turance tana nufin ƙiris)

Ƙirji -

Tana nufin sashen jikin mutum da ke tsakanin wuya da ciki.

Misali: Ya ji ciwo a ƙirji bayan ya yi gudu mai tsawo.

ENG: Chest (A turance tana nufin ƙirji)

Ƙirƙira - Tana nufin samar da wani sabon abu ko tunani ta hanyar amfani da fasaha, ilimi ko basira. Misali: Manhajar da Isa ya ƙirƙira ta ƙunshi sabon tsarin gudanar da makaranta ta yanar gizo. ENG: Invent / Create (A turance tana nufin ƙirƙira)
Ƙishi - Tana nufin jin buƙatar shan ruwa ko kuma tsananin sha’awar wani abu. Misali: Bayan doguwar tafiya a rana, matafiyin ya ji ƙishi sosai. ENG: Thirst / Craving (A turance tana nufin ƙishi)
Ƙishin-ƙishin - Tana nufin yaɗa maganganu ko labarai marasa tabbas. Misali: Na ji ƙishin-ƙishin ɗin cewa za a yi juyin mulki a ƙasar nan. ENG: Rumours / Gossip (A turance tana nufin ƙishin-ƙishin)
Ƙissa - Tana nufin labari ko bayani game da wani abu da ya faru wanda ake bayarwa domin nishaɗantarwa ko ilmantarwa. Misali: Kakarsu tana ba su ƙissa mai cike da darasi a kowanne dare. ENG: Story / Tale (A turance tana nufin ƙissa)
1 329 330 331 332