Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Stranger/Visitor - A turance yana nufin baƙo.
Misali; Jiya na yi baƙo da yamma.
HAU; Baƙo (Tana nufin wanda ba a sani ba ko wanda ya kawo ziyara)
Strive - A turance tana nufin dage.
Misali; Ya dage da karatu har sai da ya ci jarrabawarsa.
HAU; Dage (Tana nufin yin ƙoƙari matuƙa)
Struggle - A turance tana nufin daga.
Misali; An sha daga da shi kafin ya yadda a yi masa allurar.
HAU; Daga (Tana nufin gumurzu ko shan fama)
Struggle/Trouble - A turance tana nufin jidali.
Misali; Ya janyo wa kansa jidali tunda ya auri yarinyar nan.
HAU; Jidali (Tana nufin rikici ko ɗawainiya)
Stuttering/ Stammering - A turance tana nufin in'ina.
Misali; An ce shan ruwan tattabaru na sauƙaƙa in'ina.
HAU; In'ina (Tana nufin yin magana da ƙyar ko ana yi ana tsittsitsinkawa)
Suckling of Infant - A turance tana nufin jego.
Misali; Indo jego take shi yasa ba za ta bi mu ba.
HAU; Jego (Tana nufin shayar da jariri)
Sudden Attack - A turance tana nufin farmaki.
Misali; 'Yan ta'adda sun kai farmaki ga jami'an tsaro.
HAU; Farmaki (Tana nufin kai hari ba zato ba tsammani)
Suddenly - A turance tana nufin karaf.
Misali; Ta yi karaf ta kamo shi kafin ya gudu.
HAU; Karaf (Tana nufin ba zato ba tsammani)
Sufuri - Aiki ko sana'ar jigilar mutane daga wani wuri zuwa wani a mota ko jirgi.
Sum Total - A turance tana nufin jimilla.
Misali; Idan an haɗa kudina da naka za a samu jimillar dubu goma sha biyu.
HAU; Jimilla (Tana nufin sakamako na bai ɗaya)