Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Real Estate Developers Association of Nigeria (REDAN) - Ƙungiyar Masu Sana'ar Gina Mahalli Ta Najeriya
Reap - A turance tana nufin girbi.
Misali; Manoman na cikin farin ciki sakamakon lokacin girbi ya yi.
HAU; Girbi (Tana nufin kwashe amfanin gona bayan ya gama nuna)
Reason - A turance tana nufin hujja.
Misali; Sun yi rashin nasara saboda ba su da ƙwaƙƙwarar hujja a shari'ar.
HAU; Hujja (Tana nufin dalili)
Reckoning up the good and bad deeds of a person on judgement day - A turance tana nufin hisabi.
Misali; Muna fatan samun dace a ranar hisabi.
HAU; Hisabi (Tana nufin lissafa ayyukan mutum masu kyau da marasa kyau a ranar lahira)
Red - A turance tana nufin ja.
Misali; Akwai launin ja a jikin kayan da ya saka.
HAU; Ja (Tana nufin launin ja)
Red Guinea-corn -
A turance tana nufin ƙaura.
Misali: Ɗahiru ya shuka ƙaura a gonarsa wannan kakar.
HAU; Ƙaura (Tana nufin jar dawa)
Reform - A turance tana nufin jaddada.
Misali; Shugaban makarantarmu ya jaddada mana muhimmancin taron iyayen yara da za a yi gobe.
HAU; Jaddada (Tana nufin tabbatarwa)
Refuse - A turance tana nufin bola.
Misali; Motar ɗiban shara ta kwashe bolar bakin kasuwa.
HAU; Bola (Tana nufin shara ko kayan da aka gama amfani da su waɗanda za a zubar)
Refuse - A turance tana nufin ƙi.
Misali: Yaron ya ƙi cin abinci saboda ba ya jin daɗi.
HAU: Ƙi (Tana nufin rashin yarda da wani abu ko rashin amincewa da shi)
Regulation -
A turance tana nufin ƙa’ida.
Misali; Ma'aikatan suna aikinsu bisa ƙa'ida.
HAU; Ƙa'ida (Tana nufin dokoki ko tsarin da aka kafa domin tafiyar da al’amura cikin tsari)