Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Pupil/ Student - A turance yana nufin Dalibin Ƙur'ani. Misali; Abbas almajiri ne. HAU; Almajiri (Yaro ne da yake koyon karatun addini)
Puppy - A turance tana nufin kwikwiyo. Misali: Yara suna wasa da kwikwiyo a farfajiyar gida. HAU; Kwikwiyo (Tana nufin jaririn kare)
Push Forward - A turance tana nufin hankaɗa. Misali; Ya hankaɗa ta ta faɗi ƙasa. HAU; Hankaɗa (Tana nufin turawa da ƙarfi)
Push Rudely - A turance tana nufin bangaje. Misali; Musa ya bangaje abokinsa. HAU; Bangaje (Tana nufin turewa da ƙarfi)
Putting a pot on the fire - A turance tana nufin girka. Misali; Ta girka tukunya, ba za mu tafi ba sai ta sauke. HAU; Girka (Tana nufin ɗora tukunya a kan wuta)
Quantity Surveyors Registration Board Of Nigeria (QSRBN) - Hukumar Maƙiyasta Kayan Gini Ta Najeriya
Quarrel - A turance tana nufin faɗa. Misali; Ɗaliban faɗa suke bayan an tashi daga makaranta. HAU;Faɗa (Tana nufin ɗaga murya da faɗin maganaganu marasa daɗi saboda ɓacin rai)
Quarter of yard -

A turance tana nufin kwata.

Misali: Ta sayi kwata na yadi domin ɗinka gyale.

HAU; Kwata (Tana nufin rubu’in yadi ko wani ɓangare ɗaya cikin huɗu na awo)

Quick Action/ Haste - A turance tana nufin garaje. Misali; Indo tana da garaje, shi yasa ta zubar da niƙan. HAU; Garaje (Tana nufin hanzari ko sauri ko zafin nama)
Quick-Tempered - A turance tana nufin ƙufula. Misali; Ƙufula ya yi har ta kai ga ya mare shi. HAU; Ƙufula (Tana nufin saurin fushi)
1 272 273 274 275 276 332