Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Sprinkle - A turance tana nufin barbaɗa. Misali; Ya barbaɗa magani a gonarsa. HAU; Barbaɗa (Tana nufin zuzzuba abu a gurare daban-daban ba guri ɗaya ba)
Squandering - A turance tana nufin facaka. Misali; Tun da aka raba musu gado yake facaka da kuɗi. HAU; Facaka (Tana nufin kashe kuɗi ba tare da la'akari ba)
Squeeze Through - A turance tana nufin kutsa. Misali; Ya kutsa cikin taron don ya ga gwamnan garinsu. HAU; Kutsa (Tana nufin shiga da ƙyar)
Stab - A turance tana nufin caka. Misali; Mahaucin ya caka wuƙa a jikin naman ragon. HAU; Caka (Tana nufin soka abu da ƙarfi)
Standard Oraganization of Nigeria(SON) - Hukumar Inganci Ta Najeriya
State - A turance tana nufin jiha. Misali; An ƙirƙiri sabuwar jiha a ƙasar Najeriya. HAU; Jiha (Tana nufin wani yanki daga cikin ƙasa)
State Executive Council - Majilisar Zartarwa Ta Jiha
State House of Assembly - Majilisar Dokoki Ta Jiha
State Security Service/Department of State Services (SSS/DSS) - Hukumar Tsaron Sirri Ta Ƙasa
State Universal Basic Education Board (SUBEB) - Hukuamar llimin Baidaya Ta Jiha
1 271 272 273 274 275 300