Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Sweat - A turance tana nufin gumi. Misali; Yau ana zafi kowa ka gani gumi yake. HAU; Gumi (Tana nufin ruwan da yake tsattsafowa a jikin mutum ta saman fata musamman idan yana jin zafi ko ya yi gudu)
Sweet made from ground tigernuts and groundnut - A turance tana nufin daƙuwa. Misali; Zan kai wa amarya daƙuwa saboda idan ta yi baƙi ta ba su. HAU; Daƙuwa (Tana nufin alawar da ake yin ta da niƙaƙƙiyar gyaɗa da aya da sikari)
Sweet pounded millet mixed with water - A turance tana nufin gumba. Misali; An raba gumba a gidan mutuwar. HAU; Gumba (Tana nufi dakakken garin gero da sikari da ruwa)
Swell - A turance tana nufin kumbura. Misali; Ƙafarsa ta kumbura lokacin da ya ji ciwo a filin ƙwallo. HAU; Kumbura (Tana nufin ƙara girma ko tashi sakamakon bigewa ko jin ciwo)
Swollen - A turance tana nufin hulu-hulu. Misali; Idonsa ya yi hulu-hulu tun jiya saboda ciwo yake masa,. HAU; Hulu-hulu (Tana nufin kumburi sosai)
Sympathy - A turance tana nufin jaje. Misali; Shugaban ƙasa ya yi wa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa jaje. HAU; Jaje (Tana nufin taya alhini da tausayawa wanda wani abu mara daɗi ya same shi)
Sympathy/Pity - A turance tana nufin juyayi. Misali; Muna cikin juyayi sakamakon rashin da muka yi. HAU; Juyayi (Tana nufin alhini ko tausayi)
Ta’adi - Ɓarnatarwa ko tozarta dukiya, kamar kwange ko coge ko wadaka da dukiyar kasa,ko samu da ɓarnar kuɗi ba bisa ka'ida ba.
Ta’ammali - Hulɗa ko kuma yin kowace irin mu'amala da wani abu kamar miyagun kwayoyi, kama daga kan yin kwayoyin da masu siyarwa zuwa kan masu sha.
Taekwondo Federation of Nigeria (TFN) - Hukumar Wasan Taƙwando Ta Najeriya
1 275 276 277 278 279 300