Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Translation - A turance tana nufin fassara. Misali; Ya fassara littafin daga harshen larabci zuwa harshen Hausa. HAU; Fassara (Tana nufin daga wani harshe zuwa wani harshe)  
Transmission Company of Nigeria (TCN) - Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki Na Najeriya
Tree - A turance tana nufin bishiya. Misali; Idan an shuka bishiya takan ɗauki lokaci mai tsawo kafin ta girma. HAU; Bishiya (Tana nufin ice ko tsiro da yake fitowa haka kawai ko idan an shuka, yana da ganyayyaki da itatuwa a wasu lokutan)
Tree - A turance tana nufin bishiya. Misali; Wannan itacen ɗorawa ne. HAU; Itace (Tana nufin bishiya)
Tribunal - Kotun Wucin Gida
Tribunal Court - Kotun Wucin Gadi/Kotun Musamman
Truth - A turance tana nufin gaskiya. Misali; Idan mutum na faɗin gaskiya kimarsa na ƙaruwa. HAU; Gaskiya (Tana nufin abinda yake na haƙiƙa ma'ana yanda yake babu ƙari babu ragi) Kishiyarta; Ƙarya
Tsagaita - Tsahirtawa daga yin, ko barin wani abu ta hanyar taƙaitawa ko kaucewa, kamar daina yin abin da yake jawo ko haifar da asarar dukiya ko ta rayuwa.
Tsaron Sirri - Aikin tsaro ne da jami'an tsaro na farin kaya suke yi a boye domin nesa daga magauta.
Tuesday - A turance tana nufin rana ta biyu a mako. Misali; Kasuwar tana ci ranar Talata. HAU; Talata (Rana ta biyu a cikin ranakun mako)
1 252 253 254 255 256 269