Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Tax - A turance tana nufin haraji.
Misali; An tsaurara hukunci a kan masu ƙin biyan haraji a lardinmu.
HAU; Haraji (Tana nufin kuɗin da al'umma ke biya ga shugabanni wanda ake amfani da su don aiwatar da ayyukan more rayuwa)
Teach - A turance tana nufin koyarwa.
Misali; Ya karantar da mu darussa masu yawa.
HAU; Karantar (Tana nufin koyarwa)
Teachres Registration Council of Nigeria (TRCN) - Hukumar Malaman Makaranta Ta Najeriya
Teburi - Teburi wani kayan aiki ne wanda ake amfani dashi wajen rubutu ko kuma ajiye kaya akai musamman a makaranta ko kuma a gida don yin amfani.
Jam'i ; Tebura
Technology Incubation Centre (TIC) - Cibiyar Rainon Fasahar Ƙere ƙere Ta Ƙasa
Ten - A turance tana nufin goma.
Misali; Littattafai goma ne a cikin jakar.
HAU; Goma (Tana nufin lambar da ke bin bayan tara)
Termites - A turance tana nufin gara.
Misali; Gara ta cinye kujerun duk sun lalace.
HAU; Gara (Tana nufin ƙwaron da yake cinye katako)
Tertiary Education Trust Fund (TETFund) - Asusun Bunƙasa llimin Mayan Makarantu
Thanks - A turance tana nufin godiya.
Misali; Mun yi wa babanmu godiya ranar da ya siyo mana kayan salla.
HAU: Godiya (Tana nufin yabawa)
Kishiyarta; Rashin Godiya
The cult of spirit possession - A turance tana nufin bori.
Misali; 'Yan bori na gudanar da biki a duk ranar kasuwar garinmu.
HAU; Bori (Tana nufin addinin maguzanci na bautawa aljanu kafin zuwan addini musulunci)