Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Talata - Rana ce ta biyu a cikin ranakun mako.
Misali; Ana cin kasuwar duk ranar Talata.
ENG; Tuesday (A turance tana nufin rana ta biyu a mako)
Talkativeness - A turance tana nufin kauɗi.
Misali; Lantana tana da kauɗi, maganar ta duk ta cika gidan.
HAU; Kauɗi (Tana nufin yawan magana)
Tall - A turance tana nufin dogo.
Misali;Na ga wani mutum dogo a ƙofar gida.
HAU; Dogo (Tana nufin mai tsayi)
Kishiyarta; Gajere
Tanyo - Taimakawa gajiyayye ko rarrauna cikin wani al'amari, tallafawa mara karfi ga biyan wata bukata.
Tarkacen Tarihi - Karikice na abubuwan amfani da suke tabbatar da tarihi da wanzuwar wata al'umma a wani wuri.
Tasarrufi - Samarwa da juyawa ko sarrafa abu yadda ya kamata domin amfana da abin.
Taskance - Adana adadin mutane ko ma'aikatun da aka yi wa rijista karkashin wata hukuma.
Taurari - Jam'in tauraro, fitattun mutane musamman 'yankwalisa da 'yanwasa da 'yanfim da sauran mutanen da suka shahara.
Taureg - A turance tana nufin buzu.
Misali; Mai gadin gidan buzu ne, yana tare da su tsawon shekara arba'in.
HAU; Buzu (Tana nufin mazaunin ƙasashen da ke sahara kamar Niger, Mali, Algeriya da sauransu)
Tawaga - Ayari na mutane da suke nufin zuwa wani wuri domin cimma wata manufa ko aiwatar da wani aiki.