Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Things done or said intentionally - A turance tana nufin gayya. Misali; Da gayya ta yi mata magana don su yi faɗa. HAU: Gayya (Tana nufin da gangan ko ana sane)
This year - A turance tana nufin bana. Misali; Bana damina ta yi harshe, ma'ana an yi ruwa sosai. HAU; Bana (Tana nufin shekarar da ake ciki)
Thresh Grain - A turance tana nufin casa. Misali; Sai an casa shinkafar sannan za a dafa. HAU; Casa (Tana nufin cire tsaba daga cikin kwansonta, kamar shinkafa da gero da sauransu)
Throne - A turance tana nufin karaga. Misali; Sarki yana zaune a kan karaga tun safe. HAU; Karaga (Tana nufin kujerar mulki ko sarauta)
Throw powdered or ground thing into the mouth - A turance tana nufin hambuɗa. Misali; Madara ta hambuɗa a baki ta gudu. HAU; Hambuɗa (Tana nufin ɗiban abu a watsa a baki)
Thunder - A turance tana nufin tsawa yayin da ake ruwan sama.  Misali; Mun ji saukar aradu da tsakar dare ana mamakon ruwa. HAU; Aradu (Tsawa da ake yi yayin da ake ruwan sama)
Thunder Rumbling - A turance tana nufin cida. Misali; Ruwa ake da cida tun da safe har ga shi yamma ta yi. HAU; Cida (Tana nufin rugugin tsawa yayin da ake ruwan sama)
Thursday - A turance tana nufin rana ta huɗu a mako.  Misali; Aisha tana azumi duk ranar Alhamis. HAU; Alhamis  (Rana ce ta huɗu a cikin ranakun mako).
Tickling - A turance tana nufin cakulkuli. Misali; Sadiya tana yi wa ƙaninita cakulkuli yana dariya. HAU: Cakulkuli (Tana nufin taɓa kwuiɓin mutum da zimmar sa shi dariya)
Tightly - A turance tana nufin ƙam-ƙam. Misali; Ya kamata mu riƙe addini ƙam-ƙam domin inganta rayuwarmu. HAU; Ƙam-ƙam (Tana nufin riƙe abu da ƙarfi)
1 251 252 253 254 255 270