Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Tunnel/Pipe - A turance tana nufin bututu.
Misali; Mai gyaran bututun ya zo da wuri.
HAU; Bututu (Tana nufin mazurari na ruwa ko iska da sauransu)
Tusk - A turance tana nufin haure.
Misali; Da hauren giwa ake haɗa maganin.
HAU; Haure (Tana nufin haƙori)
Twenty - A turance tana nufin ishirin.
Misali; Kaji guda ishirin ya siyo don gudanar da bikin.
HAU; Ishirin (Tana nufin goma sau biyu)
Two stringed, plucked musical instrument - A turance tana nufin garaya.
Misali; Gurin ya cika da masu kiɗan garaya don bikin na 'yan bori ne.
HAU; Garaya (Tana nufin ɗaya daga cikin kayan kiɗan Hausawa na gargajiya)
Type of cloth without embroidery - A turance tana nufin gare.
Misali;Malam Audu ya sa gare.
HAU; Gare (Tana nufin rigar Hausawa mara ado)
Ulcerated Wound - A turance tana nufin gyambo.
Misali; Ai gyambon da ke ƙafarsa ya daɗe sosai.
HAU; Gyambo (Tana nufin ciwon da ba ya warkewa ko kuma ya daɗe bai warke ba)
Uncompleted Building - A turance tana nufin kango.
Misali; Har yanzu ginin kango ne ba a ƙarasa ba.
HAU; Kango (Tana nufin ginin da ba a kammala ba)
Understand - A turance tana nufin fahimta.
Misali; Ɗaliban suna da fahimta ƙwarai da gaske.
HAU; Fahimta (Tana nufin ganewa)
Kishiyarta; Rashin Fahimta
Understand - A turance tana nufin gane.
Misali; Ina fatan kun gane abinda nake nufi?
HAU; Gane (Tana nufin fahimta)
Kishiyarta; Rashin Ganewa
Ungrateful - A turance tana nufin butulu
Misali; Cindo butulu ne saboda ya butulcewa maigidansa a kasuwa.
HAU; Butulu (Tana nufin wanda yake manta alkahairin da aka yi masa)