Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Pull out suddenly with force - A turance tana nufin fincika.
Misali; Ta tsinka jakar da ta fincika.
HAU; Fincika (Tana nufin jan abu da ƙarfi)
Pull/Drag - A turance tana nufin ja.
Misali; Ya ja igiyar da ƙarfi shi yasa ta tsinke.
HAU; Ja (Tana nufin janyowa)
Pumpkin - A turance tana nufin kabewa.
Misali; Tuwon shinkafa da miyar kabewa za a dafa.
HAU; Kabewa (Tana nufin nau'in itaciya mai ƙunshe da sinadaren da jiki ke buƙata, ana amfani da ita wajen yin miya da lemo da sauransu)
Pupil/ Student - A turance yana nufin Dalibin Ƙur'ani.
Misali; Abbas almajiri ne.
HAU; Almajiri (Yaro ne da yake koyon karatun addini)
Push Forward - A turance tana nufin hankaɗa.
Misali; Ya hankaɗa ta ta faɗi ƙasa.
HAU; Hankaɗa (Tana nufin turawa da ƙarfi)
Push Rudely - A turance tana nufin bangaje.
Misali; Musa ya bangaje abokinsa.
HAU; Bangaje (Tana nufin turewa da ƙarfi)
Putting a pot on the fire - A turance tana nufin girka.
Misali; Ta girka tukunya, ba za mu tafi ba sai ta sauke.
HAU; Girka (Tana nufin ɗora tukunya a kan wuta)
Quantity Surveyors Registration Board Of Nigeria (QSRBN) - Hukumar Maƙiyasta Kayan Gini Ta Najeriya
Quarrel - A turance tana nufin faɗa.
Misali; Ɗaliban faɗa suke bayan an tashi daga makaranta.
HAU;Faɗa (Tana nufin ɗaga murya da faɗin maganaganu marasa daɗi saboda ɓacin rai)
Quick Action/ Haste - A turance tana nufin garaje.
Misali; Indo tana da garaje, shi yasa ta zubar da niƙan.
HAU; Garaje (Tana nufin hanzari ko sauri ko zafin nama)