Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Kwakwazo - Tana nufin hayaniya da hayagaga. Misali; Tun safe Lami take kwakwazo don an ɗauke mata kuɗi a gidan suna. ENG; Loud Fuss (A turance tana nufin kwakwazo)
Kwal - Tana nufin gawayi. Misali; Sana'ar siyar da kwal ta karɓi Ado matuƙa. ENG; Coal (A turance tana nufin kwal)
Kwala - Tana nufin wuyan riga irin ta Bature. Misali; Yana sanye ne da riga mai kwala launin shuɗi. ENG; Collar (A turance tana nufin kwala)
Kwalaba - Tana nufin mazubin da aka yi shi da gilashi. Misali; Ana auna mai da kwalaba da kuma gwangwani. ENG; Bottlle (A turance tana nufin kwalaba)
Kwaleji - Tana nufin makarantar gaba da firamare ko gaba da sakandire. Misali; Duk wanda zai shiga kwaleji sai ya yi jarrabawa. ENG; College (A turance tana nufin kwaleji)
Kwaleji - Tana nufin makaranta musamman ta gaba da sakandire. Misali; Idan matasa suka shiga kwaleji suna jin kansu. ENG; College (A turance tana nufin kwaleji)
Kwalekwale - Tana nufin ƙaramin jirgin ruwa. Misali; Ba a zuwa ƙauyen sai an hau kwalekwale. ENG; Canoe (A turance tana nufin kwalekwale)
Kwalli - Tana nufin nau'in abin ado da ake sa wa ido don ƙara masa kyau da ƙwari. Misali: Kwaliiya ta ba ta cika sai na sa kwalli a idona. ENG: Antimony (A turance tana nufin kwalli)  
Kwalliya - Tana nufin yin ado ko ƙawatawa ta hanyar sanya kayan ado. Misali: 'Yan matan sun yi kwalliya za su gidan biki. ENG; Beautification/Make-up (A turance tana nufin kwalliya)
Kwamanda - Tana nufin shugaba ko jagora ko mai ba da umarni. Misali; Ya samu ƙarin matsayi zuwa kwamanda a aikinsa na soja. ENG; Commander (A turance tana nufin kwamanda)
1 207 208 209 210 211 337