Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Kushin - Tana nufin kujerar bature.
Misali; Hedimasta yana zaune a kan kushin ɗin ofishinsa a lokacin da muka kai masa ziyara.
ENG; Cushion (A turance tana nufin kushin)
Kuskure - Tana nufin yin abu ba daidai ba.
Misali; Idan mutum ya yi kuskure ya kamata a yi masa afuwa.
ENG; Failure (A turance tana nufin kuskure)
Kusu - Tana nufin ɓera.
Misali; Na ga kusu a cikin ɗakin ajiya, dole sai mun sa magani.
ENG; Rat/Mouse (A turance tana nufin kusu)
Kusurwa - Tana nufin kwana.
Misali; Na ajiye adakar a kusurwar ɗakin da muke kwana.
ENG; Corner (A turance tana nufin kusurwa)
Kutsa - Tana nufin shiga da ƙyar.
Misali; Ya kutsa cikin taron don ya ga gwamnan garinsu.
ENG; Squeeze Through (A turance tana nufin kutsa)
Kuturta - Tana nufin lalurar da ke sa ƙuraje a jiki, ta canja siffar mutum gaba ɗaya kuma yatsu su lanƙawashe.
Misali; Gwamnati ta daɗe da yaƙar cutar kuturta a ƙasar nan.
ENG; Leprosy (A turance tana nufin kuturta)
Kuturu - Tana nufin mai ɗauke da lalurar kuturta.
Misali; Ya ba wa kuturu sadaka a hanyarsa ta zuwa kasuwa.
ENG; Leper (A turance tana nufin kuturu)
Kuwwa - Tana nufin ƙara.
Misali; Yara na waje suna kuwwa saboda saukar ruwan sama na farko.
ENG; Shouting (A turance tana nufin kuwwa)
Kuyanga - Tana nufin baiwa mace.
Misali; Mallakar kuyanga sai masu hannu da shuni.
ENG; Female Slave (A turance tana nufin kuyanga)
Kuza - Tana nufin zuba ruwa da yawa.
Misali; Hindatu ta kuza ruwa a cikin shinkafar shi yasa ta yi luguf.
ENG; Pour much water (A turance tana nufin kuza)