Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Kurkure - Tana nufin zuba ruwa a jujjuya shi a cikin baki da zimmar ɗurayewa. Misali; Idan za a yi alwala ana kurkure baki sau uku ne. ENG; Rinse (Mouth) (A turance tana nufin kurkure)
Kurma - Tana nufin mai ɗauke da lalurar rashin ji. Misali; Tun yana yaro ya zama kurma sakamakon ciwon baƙon dauro da ya yi. ENG: Deaf person (A turance tana nufin kurma)
Kurmi - Tana nufin ƙungurmin daji. Misali; Jami'an tsaro sun kame ɓarayin da ke kurmi gaba ɗaya. ENG; Thick Forest (A turance tana nufin kurmi)
Kurna - Tana nufin bishiya mai ƙaya mau ɗauke da ƙananan 'ya'ya masu zaƙi waɗanda ake sha. Misali; 'Ya'yan kurna suke sha kullum idan sun je makaranta. ENG; A thorny tree with edible berries (A turance tana nufin kurna)
Kurtu - Tana nufin ƙaramin mazubi na duma. Misali; Maharazu ya zuba tawada a cikin kurtu. ENG; Small Round Gourd (A turance tana nufin kurtu)
Kurum - Tana nufin kawai. Misali; Kwano ɗaya kurum ta isa kowa ya ƙoshi. ENG; Only (A turance tana nufin kurum)
Kururuwa - Tana nufin ihu da ƙarfi. Misali; Sadiƙ yana da rowa idan aka ɗauki abinsa kururuwa yake. ENG; Shouting (A turance tana nufin kururuwa)
Kusa - Tana nufin dab da. Misali; Ana siyar da wainar gero a kusa da gidanmu. ENG; Near (A turance tana nufin kusa)
Kushe - Tana nufin faɗar aibu ko ƙaƙalo laifin abu. Misali; Duk yanda abu ya kai da kyau mahassada sai sun kushe shi. ENG; Find Fault (A turance tana nufin kushe)
Kushewa - Tana nufin kabari. Misali; An kai ta kushewa tun safe da aka yi jana'izarta. ENG; Grave (A turance tana nufin kushewa)
1 204 205 206 207 208 337