Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Kura - Tana nufin wata dabbar daji mai cin ɗanyen nama.
Misali; Mafarautan sun kamo kura.
ENG; Hyena (A turance tana nufin kura)
Kuratandu - Tana nufin mazubin kwalli wato mazubin da ake adana kwalli a ciki.
Misali; Inna Hajjo ta kawo wa mai jego kyautar kurantandu cike da farin kwalli.
ENG: Small hide container (A turance tana nufin kuratandu)
Kurciya - Tana nufin ƙaramar tsuntsuwa.
Misali; Kukan kurciya jawabi ne, mai hankali ke ganewa.
ENG; Small Dove (A turance tana nufin kurciya)
Kure - Tana nufin namijin kura.
Misali; Auwalu ya kamo kure, da shi yake wasa ranar kasuwa.
ENG; Male Hyena (A turance tana nufin kure)
Kurege - Tana nufin wata dabba mai kama da zomo.
Misali; Ado ya bi kurege har cikin raminsa ya kamo shi.
ENG; Ground Squirrel (A turance tana nufin kurege)
Kurga - Tana nufin koren kashi mai kumfa wanda yaran da ake shayarwa ke yi.
Misali; Tana shirin yaye ɗanta ya fara kurga.
ENG; Diarrhoe In Children (A turance tana nufin kurga)
Kuri - Tana nufin cika baki ko kambama kai.
Misali; Safiyanu ya cika kuri, amma ana taɓa shi zai fara kuka.
ENG; Boasting (A turance tana nufin kuri)
Kurkudu - Tana nufin wani ƙwaro da yake fitowa a cikin rairayi.
Misali; Yaran sun kamo kurkudu a lokacin da suke wasa.
ENG; Sand Lice (A turance tana nufin kurkudu)
Kurkuku - Tana nufin inda ake ajiye masu laifi, waɗanda aka yankewa hukunci da masu jiran hukunci.
Misali; Jami'an sun tafi da masu laifin kurkuku.
ENG; Prison (A turance tana nufin kurkuku)
Kurkunu - Tana nufin cutar fata mai sanya ƙuraje.
Misali; An yi nasarar kawar da cutar kurkunu a Najeriya.
ENG; Guinea-worm (A turance tana nufin kurkunu)