Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Kullum - Tana nufin kowacce rana. Misali; Mukan yi salla sau biyar a kullum. ENG; Every Day (A turance tana nufin kullum)
Kulob - Tana nufin ƙungiya. Misali; Jibrin ɗan ƙungiyar Hausa ne a makaranta. ENG; Club (A turance tana nufin kulob)
Kulɓa - Tana nufin dabba mai kama da ƙadangare amma jikinta yana da santsi kuma tana da launuka daban-daban, tana rayuwa a cikin ciyayi. Misali; Na ga kulɓa a filin da muke wasa a makaranta. ENG; Skink Lizard (A turance tana nufin kulɓa)
Kuma - Tana nufin sake yi ko maimaitawa. Misali; Yanzu zazzaɓi ba ya jin magani ko kin sha sai kin kuma sha. ENG; Repeat (A turance tana nufin kuma)
Kumama - Tana nufin mutum mai saurin jin sanyi. Misali; Sadiq kumama ne, ko yaya aka yi ruwa sai ya sa rigar sanyi. ENG; Person of weak physical constitution (A turance tana nufin kumama)
Kumatu - Tana nufin jam'in kunci wato gefen fuska na hagu ko na dama. Misali; Fauziya ta shafa hoda a kumatu. ENG; Cheeks (A turance tana nufin kumatu)  
Kumbon Sadarwa - Tauraron dan'adam, wato kumbon da ake harbawa zuwa sararin sama ko wata duniyar domin sadarwa, musamman ta radiyo da waya da tattaro bayanai.
Kumbura - Tana nufin ƙara girma ko tashi sakamakon bigewa ko jin ciwo. Misali; Ƙafarsa ta kumbura lokacin da ya ji ciwo a filin ƙwallo. ENG; Swell (A turance tana nufin kumbura)
Kumfa - Tana nufin wani farin abu mara nauyi da yake tasowa idan an kaɗa sabulu a ruwa ko kuma idan an juye lemo mai gas ko a kogi idan ruwa ya hautsine. Misali; Ai dole wankin nan ya fita don sabulun yana da kumfa sosai. ENG; Foam/Froth (A turance tana nufin kumfa)
Kumurci - Tana nufin baƙin maciji mai dafi. Misali; Kumurci ya sari kaka a gona. ENG; Black-hooded Cobra (A trurance tana nufin kumurci)
1 201 202 203 204 205 337