Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Kuje - Tana nufin jin ciwo a saman fata.
Misali; Amir ya faɗi ya kuje a gwuiwa.
ENG; Scratch (A turance tana nufin kuje)
Kujera - Tana nufin abin da ake zama a kai.
Misali; Inna ta siyo sabuwar kujera.
ENG; Chair (A turance tana nufin kujera)
Kuka - Tana nufin koren ganyen bishiyar da ake amfani da shi don yin miya, yana da sinadarai masu matuƙar amfani a jiki.
Misali; Miyar kuka na ɗaya daga cikin miyoyin Hausawa na gargajiya.
ENG; Baobab Tree (A turance tana nufin kuka)
Kuka - Tana nufin zubar hawaye daga idanu sakamakon murna ko ɓacin rai.
Misali; Safiya ta sha kuka lokacin da mahaifinta ya rasu.
ENG; Crying (A turance tana nufin kuka)
Kuku - Tana nufin wanda yake aikin dafa abinci.
Misali; Gidan attajirai ne ake ajiye kuku.
ENG; Cook (A turance tana nufin kuku)
Kukuma - Tana nufin ɗaya daga cikin kayan kaɗe-kaɗe na gargajiya.
Misali; Makaɗan kukuma suna da baiwa ta musamman.
ENG; Small one stringed bowed musical instrument (A turance tana nufin kukuma)
Kula - Tana nufin mayar da hankali a kan abu.
Misali; Idan za ki tsallaka titi ki kula saboda motoci na wucewa da gudu.
ENG; Pay Attention (A turance tana nufin kula)
Kule - Tana nufin mage.
Misali; Gidansu Hanan suna da ƙaton kule.
ENG; Cat (A turance tana nufin mage)
Kulki - Tana nufin gajeren sanda mai kauri wanda 'yan doka suke riƙewa.
Misali; Ɗan dokar na riƙe da kulki lokacin da suka je kama ɓarayin.
ENG; Cudgel (A turance tana nufin kulki)
Kulle - Tana nufin rufewa.
Misali; Lokacin da muka je an kulle ƙofar saboda mun makara.
ENG; Lock (A turance tana nufin kulle)