Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Koyar - Tana nufin sanar da mutum ilimi. Misali; Malam Musa Ya koyar da mu darasin lissafi. ENG; Teach (A turance tana nufin koyar)
Koyaushe - Tana nufin kowane lokaci. Misali; Kakarmu tana ibada a koyaushe. ENG; Always (A turance tana nufin koyaushe)
Koyaya - Tana nufin duk ƙaranci. Misali; Koyaya mutum ya samu ilimi zai masa amfani. ENG; No Matter How (A turance tana nufin koyaya)
Koyi - Tana nufin kwaikwaya ko yin abinda wani ya yi. Misali; Koyi da annabawa kyakkyawar ɗabi'a ce. ENG; Imitate (A turance tana nufin koyi)
Koɗe - Tana nufin canja yanayi ko launi musamman sakamakon jin jiki.  Misali; Atamfar ta koɗe saboda ta sha wanki a kai a kai. ENG; Fade (A turance tana nufin koɗe)
Kucaki - Tana nufin mutum mara tsafta. Misali; Wani kucaki ne a bakin kasuwa yake siyar da gwangwanaye. ENG; Slovenly Person (A turance tana nufin kucaki)
Kudu - Tana nufin wani ɓangare daga cikin ɓangarori. Misali; Gabas ake kallo idan za a yi salla ba kudu ba. ENG; South (A turance tana nufin kudu)
Kududdufi - Tana nufin ƙaton rami da ake samu a ƙauyuka da bayan gari, idan damina ta zo yakan cika da ruwa. Bayan damina kuma akan ɗibi yashi ko ƙasar gurin a yi amfani da ita. Misali; Kafin mutane su yi gine-gine ƙaton kududdufi ne a gurin. ENG; Burrow-Pit (A turance tana nufin kududdufi)
Kufai - Gurbi na ramuka ko koguna ko gine-ginen da suke nuna cewar mutane sun taba wanzuwa/zama a wurin a  zamunnan  baya.
Kufta - Tana nufin taguwa mai tsayin da ya haura gwuiwa, tana da aiki a wuyan da bakin aljihu da kuma hannun rigar. Misali; Ɗinkin kufta ya yi tsada ba kowa ne yake iya yi ba. ENG; A three-quarter length taguwa with embroidery around the neck and sleeves (A turance tana nufin kufta)
1 199 200 201 202 203 337