Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Kiɗime - Tana nufin gigicewa ko shiga wani hali. Misali; Duk sun kiɗime saboda tashin hankali. ENG; Confused/Flustered (A turance tana nufin kiɗime)  
Knee - A turance tana nufin gwiwa. Misali; Ciwon gwiwa yake yi tunda shekarunsa suka ja. HAU; Gwiwa (Tana nufin sashen jiki da ke tsakanin ƙafa da cinya)
Kneel with front elbows on ground - A turance tana nufin gurfana. Misali; Masu laifin sun gurfana a gaban alƙali. HAU; Gurfana (Tana nufin durƙusawa a kan gwuiwa biyu)
Knowledge - A turance tana nufin ilimi. Misali; Allah ya yi masa baiwar ilimi ƙwarai da gaske. HAU; Ilimi (Tana nufin sani)
Kofato - Tana nufin ƙafar dabba kamar saniya ko akuya ko doki. Misali; Na ga shatin kofato da alama doki ya bi ta nan gurin. ENG; Hoof (A turance tana nufin kofato)
Kogi - Tana nufin ruwa mai gudana. Misali; An tsinci jariri a bakin kogi ranar Asabar. ENG; River (A turance tana nufin kogi)
Kogo - Tana nufin wani wawakeken rami da ke jikin bishiya kamar ta kuka, tsamiya da sauransu. Misali; Karnukan sun shige cikin kogon bishiya a gonar da ke bayan gari. ENG; Hollow of tree (A turance tana nufin kogo)
Kokawa - Tana nufin ɗaya daga cikin wasannin gargajiya, inda maza biyu ke doke-doke a tsakaninsu har a kayar da ɗaya. Misali; Su Lado sun tafi kallon kokawa a dandali. ENG; Wrestling (A turance tana nufin kokawa)
Koko - Tana nufin abin sha da ake yi da gero, ana dama shi da tafasasshen ruwa kamar kunu. Misali; Koko da ƙosai ɗaya ne daga cikin abincin karin kumallon Hausawa. ENG; Millet Porridge (A turance tana nufin koko)
Koko-koke - Tana nufin jam'in kuka. Misali; Na jiyo ana ta koke-koke a gidan mutuwar, Allah ya gafarta masa da rahama. ENG; Cries (A turance tana nufin koke-koke)
1 197 198 199 200 201 337