Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Kokwanto - Tana nufin yin wasi-wasi ko tunanin abu daidai ne ko ba daidai ba, zai yiwu ko ba zai yiwu ba.
Misali; Tun safe nake kokwanton fita, kar in fita ruwa ya sakko don akwai gagarimin hadari.
ENG; Doubt (A turance tana nufin kokwanto)
Kolanut - A turance tana nufin goro.
Misali; An raba goro a gurin ɗaurin auren.
HAU; Goro (Tana nufin ɗan itaciya da ake ci mai ƙunshe da muhimman abubuwa masu inganci)
Kolo - Tana nufin nau'in abin kiɗa mai kama da jauje.
Misali; Malam Habu makaɗin kolo ne sama da shekaru ashirin da suka wuce.
ENG; Drum similar to jauje (A turance tana nufin kolo)
Koma - Tana nufin abin da masunta suke amfani da shi wajen kama kifi.
Misali; Akwai koma a cikin jakar da yake tafiya SU da ita.
ENG; Fishing Net (A turance tana nufin koma)
Kora - Tana nufin nau'in cutar fata da yake fitowa a kai.
Misali; Yana da kora, idan ka sa hularsa za ka iya ɗauka kuma lalura ce mai wuyar sha'ani.
ENG; Scalp Disease (A turance tana nufin kora)
Kore - Tana nufin launi.
Misali; Kayan makarantarsu kore ne.
ENG; Green (A turance tana nufin kore)
Koshi - Tana nufin cikar ciki bayan cin abinci sosai.
Misali: Ya ƙoshi sosai bayan ya ci tuwo da miya.
ENG: Be Replete (A turance tana nufin koshi)
Kotso - Tana nufin ɗaya daga cikin kayan kiɗan Hausawa.
Misali; Ya daɗe yana kaɗa kotso a ƙauyensu.
ENG; Open-ended variable tone drum which is beaten with fingers (A turance tana nufin kotso)
Kotu - Tana nufin gurin da ake gudanar da shari'a.
Misali; Lauyoyin sun fito harabar kotu domin su huta kafin shiga shari'a ta gaba.
ENG; Court (A turance tana nufin kotu)
Kowa - Tana nufin mutane baki ɗaya.
Misali; Kowa zai iya neman tallafin da gwamnati take bayarwa.
ENG; Everyone (A turance tana nufin kowa)