Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Kintsa - Tana nufin tattara kaya guri ɗaya. Misali; Kar ki fita sai kin kintsa ɗakin tunda kin bari yara sun hargitsa shi. ENG; Tidy Up (A turance tana nufin kintsa)
Kintsattse - Tana nufin mutum mai kamala da nutsuwa. Misali; Ai da ganinsa an ga kintsattse, don kamanninsa sun nuna haka. ENG; Polite (A turance tana nufin kintsattse)
Kirari - Tana nufin maganganun da ake yi wa mutum ko mutane don kwarzantawa ko kambamawa. Misali; A kodayaushe akan yi wa mafarauta kirari kafin su tafi farauta. ENG; Praise (A turance tana nufin kirari)
Kirci - Tana nufin wasu ƙuraje masu matuƙar ƙaiƙayi da ke fitowa a fata sakamakon rashin tsabta.  Misali; Abin da yasa almajirai ke yin kirci shi ne rashin wanka. ENG; Eczema (A turance tana nufin kirci)
Kirista - Tana nufin mabiya addinin kiristanci wato ahalil kitabi. Misali; Makociyata kirista ce, kuma muna zaman lafiya sosai. ENG; Christian (A turance tana nufin kirista)
Kirki - Tana nufin kyautatawa ko hali mai kyau. Misali; Yin tarayya da mutanen kirki na sa mutum ya zama mai nagarta. ENG; Kindness (A turance tana nufin kirki)
Kirsimeti - Tana nufin bikin zagayowar ranar haihuwar Yesu Almasihu. Misali; Kiristoci na bikin kirsimeti a duk ranar 25 ga watan Disamba. ENG; Christmas (A turance tana nufin kirsimeti)  
Kirɓa - Tana nufin daka abu sosai a cikin turmi. Misali; Za mu kirɓa sakwara a ranar bikin da yardar Allah. ENG; Pound (A turance tana nufin kirɓa)
Kisa - Tana nufin ɗaukar rai. Misali; 'Yan ta'adda sun mayar da kisa ba komai ba a Najeriya. ENG; Killing (A turance tana nufin kisa)
Kishi - Tana nufin sosuwar zuciya da ɓacin ran da suke jawo fushi, a dalilin tarayyar da wani ya yi da wani, a kan abin da wanin ya keɓanta da son sa koma mallakarsa. Misali; Matan wannan zamani na da matuƙar kishi wanda ya saɓawa shari'a. ENG; Jealousy (A turance tana nufin kishi)
1 195 196 197 198 199 337