Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Kilaki - Tana nufin (karuwa) mace mai zaman kanta. Misali; Kowa ya san tsohuwar kilaki ce, sai dai mu ce Allah ya shirye mu duka. ENG; Harlot (A turance tana nufin karuwa)
Kilisa - Tana nufin hawa dokuna don nishaɗi. Misali; An shirya kilisa a bikin angwancin Abdullahi. ENG; Horse-riding for pleasure (A turance tana nufin kilisa)
Kilishi - Tana nufin nama wanda aka sarrafa shi da kayan ƙamshi kuma aka busar da shi a rana. Misali; A Unguwar Agadasawa ana siyar da kilishi da dambun nama. ENG; Meat coated with spices and dried in the sun (A turance tana nufin kilishi)
Killing - A turance tana nufin kisa. Misali; 'Yan ta'adda sun mayar da kisa ba komai ba a Najeriya. HAU; Kisa (Tana nufin ɗaukar rai)
Kilogiram - Tana nufin ma'aunin nauyi. Misali; Nauyin buhun shinkafa kilogiram hamsin ne. ENG; Kilogram (A turance tana nufin kilogiram)
Kilogram - A turance tana nufin kilogiram. Misali; Nauyin buhun shinkafa kilogiram hamsin ne. HAU; Kilogiram (Tana nufin ma'aunin nauyi)
Kilometer - A turance tana nufin kilomita. Misali; Nisan Jihar Kano zuwa jihar Legas ya kai kusan kilomita dubu. HAU; Kilomita (Tana nufin ma'aunin nisan tafiya)
Kilomita - Tana nufin ma'aunin nisan tafiya. Misali; Nisan Jihar Kano zuwa jihar Legas ya kai kusan kilomita dubu. ENG; Kilometer (A turance tana nufin kilomita)
Kindirmo - Tana nufin Nonon da ya kwana ya yi kauri. Misali; Ina son shan kindirmo da safe. ENG; Youghurt (A turance tana nufin kindirmo)
Kindness - A turance tana nufin kirki. Misali; Yin tarayya da mutanen kirki na sa mutum ya zama mai nagarta. HAU; Kirki (Tana nufin kyautatawa ko hali mai kyau)
1 194 195 196 197 198 337