Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Kerosene - A turance tana nufin kananzir. Misali; Zamani ya sa an dena amfani da kananzir sosai. HAU; Kananzir (Tana nufin makamashin da ake amfani da shi wajen girki da kunna fitila)
Keso - Tana nufin tsohuwar tabarmar kaba. Misali; An ɗora buhun geron a kan keso. ENG; Worn-out palm-leaf mat (A turance tana nufin keso)
Kettle - A turance tana nufin buta. Misali; Na siyo sabuwar buta a kasuwar da na je. HAU; Buta (Tana nufin mazubin ruwa musamman don yin alwala)
Kewa - Tana nufin son gani ko kasancewa da wanda ba ya kusa ko ya rasu. Misali; Idan mutum ya rasu akan kasance cikin kewarsa a kodayaushe. ENG; Missing Someone (A turance tana nufin kewa)
Keɓe - Tana nufin warewa gefe. Misali; Sun keɓe suna tattaunawa saboda batun yana da muhimmanci. ENG; Set Aside (A turance tana nufin keɓe)
Khaki Cloth - A turance tana nufin kaki. Misali; Dole ne ka ji tsoron mai kaki don ka san soja ba abin wasa ba ne. HAU; Kaki (Tana nufin kayan sojoji)
Kibiya - Tana nufin abin da ake ƙerawa, ana mafani da ita don yin harbi. Misali; Jarumin ya harba kibiya a ƙirjin dokin. ENG; Arrow (A turance tana nufin kibiya)
Kicin - Tana nufin ɗakin girki. Misali; Hamida tana taya Umma girki a kicin. ENG; Kitchen (A turance tana nufin kicin)
Kidney - A turance tana nufin ƙoda. Misali: Likita ya ce alamomin lalurarsa na kama da na ciwon ƙoda. HAU: Ƙoda (Tana nufin wata muhimmiyar gaɓa da ke cikin ciki wadda ke tace jini tare da fitar da datti ta fitsari)
Kifi - Tana nufin ɗaya daga cikin dabbobin ruwa. Misali; San'ar kifi sana'a ce mai albarka. ENG; Fish (A turance tana nufin kifi)
1 193 194 195 196 197 337