Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Katse - Tana nufin yankewa ko tsayar da abu.
Misali; Idan aka katse min bacci ciwon kai yake sa ni.
ENG; Cut Off (A turance tana nufin katse)
Kauci - Tana nufin wani tsiro da yake fitowa a jikin bishiya, kuma yana fitowa ne sakamakon sauka da tsuntsaye ke yi daga wata bishiyar zuwa wata.
Misali; Ana amfani da kauci wajen magungunan cututtuka da dama.
ENG; A parasitic plant which grows on trees (A turance tana nufin kauci)
Kauri - Tana nufin abin da ba siriri ba ko kuma wanda ba ruwa-ruwa ba.
Misali; Kunun da ta dama ya yi kauri sosai, sai an ƙara ruwa.
ENG; Thickness (A turance tana nufin kauri)
Kauɗi - Tana nufin yawan magana.
Misali; Lantana tana da kauɗi, maganar ta duk ta cika gidan.
ENG; Talkativeness (A turance tana nufin kauɗi)
Kawai - Tana nufin kaɗai.
Misali; Kuɓewa kawai na siyo da na je kasuwa.
ENG; Only (A turance tana nufin kawai)
Kawaici - Tana nufin ɗauke kai ko yin shiru a kan abinda ya kama mutum ya yi magana amma sai ya yi shiru.
Misali; Laure tana da kawaici shi yasa suke mata abinda suka ga dama.
ENG; Reticence (A turance tana nufin kawaici)
Kawali - Tana nufin wanda yake haɗa mata masu zaman kansu da maza, kuma sukan ba shi wani kaso daga cikin kuɗin da suka samu.
Misali; Cin fuska ne a ce wa mutum kawali don ba sana'ar mutanen kirki ba ce.
ENG; Pimp (A turance tana nufin kawali)
Kawu - Tana nufin wa ko ƙanin mahaifi ko mahaifiya.
Misali; A cikin mutanen da suka zo har da Kawu, shi ne ma ya jagoranci tafiyar.
ENG; Uncle (A turance tana nufin kawu)
Kawuna - Tana nufin jam'in kai.
Misali; 'Yan gidan manyan kawuna garesu.
ENG; Heads (A turance tana nufin kawuna)
Kaya - Tana nufin abubuwa da yawa.
Misali; Motar ɗaukan kaya yake ja yanzu.
ENG; Goods/Loads (A turance tana nufin kaya)