Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Karsana - Tana nufin matashiyar saniya wadda ba ta taɓa haihuwa ba.
Misali; Naman karsana yana da taushi da sauƙin dahuwa.
ENG; Young cow who has not yet given birth (A turance tana nufin karsana)
Kartagai - Shugabannin caca, wanda suka mallaki kaya da ma wuri ko gidajen yin cacar.
Karuwa - Tana nufin mace mai zaman kanta.
Misali; Ku karanta ƙissar karuwa da karen da ta ba wa ruwa, akwai darasi.
ENG; Prostitute (A turance tana nufin karuwa)
Karya - Tana nufin macen kare.
Misali; Wata karya ce ta haihu a bayan layinmu.
ENG; Bitch (A turance tana nufin karya)
Karya - Tana nufin ɓalla abu ko raba shi gida biyu.
Misali; Yaran sun karya kujerun ajin su.
ENG; Break (A turance tana nufin karya)
Karɓa - Tana nufin riƙewa ko yarda.
Misali; Duk hukuncin da aka yanke masa dole ya karɓa don ya yi gagarumin laifi.
ENG; Accept/Received (A turance tana nufin karɓa)
Kasada - Tana nufin yin abu mai hatsari ko ganganci.
Misali; Bin hanyar nan kasada ne saboda akwai 'yan ta'adda a wajen.
ENG; Risk (A turance tana nufin kasada)
Kasala - Tana nufin mutuwar jiki ko rashin jin ƙarfin jiki.
Misali; Jin kasala na ɗaya daga cikin alamomin juna biyu.
ENG; Lack of Energy (A turance tana nufin kasala)
Katifa - Tana nufin abin kwanciya mai laushi.
Misali; An siyowa amarya sabuwar katifa.
ENG; Mattress (A turance tana nufin katifa)
Katsalandan - Tana nufin shiga abin da bai shafi mutum ba ko shisshigi.
Misali; Makwabcinsa yana yawan yi masa katsaladan a al'amuran shi.
ENG; Intrusiveness (A turance tana nufin katsalandan)