Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Karin Magana - Tana nufin zance na hikima mai ƙunshe da nuni ko habaici wanda ake yi don azanci ko huce haushi. Misali; Darasin da malamin Hausa ya koyar yau shi ne karin magana. ENG; Proverb (A turance tana nufin karin magana)
Karkanda - Tana nufin ɗaya daga cikin dabbobin daji mai matuƙar ƙarfi. Misali; Ba a ganin karkanda sai a ƙungurmin daji. ENG; Rhinoceros (A turance tana nufin karkanda)
Karkara - Karkara wani yanki ne na gari wanda yake ke6antaccen waje ne da yakje da karancin jama'a da kuma yake da yawan gonaki da filaye.
Karkara - Tana nufin ƙauye. Misali; Mutanen karkara suna da karamci matuƙa. ENG; Rural Area (A turance tana nufin karkara)
Karkarwa - Tana nufin rawar da jiki yake yi sakamakon zazzaɓi ko jin sanyi. Misali; Idan ba ka sa rigar sanyi ba za ka yi karkarwa saboda yau akwai matuƙar sanyi. ENG; Shivering (A turance tana nufin karkarwa)
Karkashi - Tana nufin ganyen da ake miya da shi, yana da yauƙi sosai. Misali; Tuwo zan dafa da miyar karkashi yau. ENG; Herb used in making soup (A turance tana nufin karkashi)
Karmami - Tana nufin ganyen dawa. Misali; Da ya bi shi da gudu, cikin karmami ya shige. ENG; Leaves of Guinea-corn (A turance tana nufin karmami)
Karo - Tana nufin haɗuwar ba-zata. Misali; Karo na yi da bango saboda duhu, shi yasa goshi na ya kumbura. ENG; Collision (A turance tana nufin karo)  
Karo-karo - Tana nufin haɗaka ma'ana a haɗo wancan da wannan guri ɗaya. Misali; Za mu yi masa karo-karo ya siyi babur ya kama sana'a. ENG: Seeking contribution from various people (A turance tana nufin karo-karo)
Karofi - Tana nufin rami mai ɗauke da ruwan da ake rina tufafi. Misali; Na taɓa ganin karofi a marinar da ke unguwar Ƙofar Mata. ENG; Dye-pit (A turance tana nufin karofi)
1 189 190 191 192 193 337