Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Kwamishina - Tana nufin jami’i ko shugaba da gwamnati ta naɗa domin kula da wani ɓangare ko ma’aikata. Misali; An naɗa shi kwamishina a ma’aikatar ilimi. ENG; Commissioner (A turance tana nufin kwamishina)
Kwana -

Tana nufin kusurwa ko gefen wani wuri, musamman inda ɓangarori biyu suka haɗu.

Misali; Shagon Alhaji Manu na da kwana guda uku.

ENG; Corner (A turance tana nufin kwana)

Kwana -

Tana nufin yin dare ko kwashe dare a wani wuri har zuwa wayewar gari.

Misali: Matafiyan sun kwana a Kano kafin su ci gaba da tafiyarsu.

ENG: Spend the night (A turance tana nufin kwana).

Kwance - Tana nufin kayan da aka taɓa amfani da su a baya sannan aka bayar ko aka siyar. Misali:Ya sayi kayan kwance a kasuwar Sabon Gari Market saboda sun fi araha. ENG: Second-hand goods (A turance tana nufin kwance).
Kwance - Tana nufin warware abin da aka ɗaure ko sakin abu daga matsewa ko ƙulli. Misali; Ya kwance igiyar da aka ɗaure a jikin ƙofa. ENG; Untie (A turance tana nufin kwance)
Kwanciya -

Tana nufin shimfiɗa jiki ko hutawa a kan gado, tabarma ko wani wuri.

Misali; Bayan ya gama aiki ya samu gurin kwanciya domin ya huta.

ENG; Lying down (A turance tana nufin kwanciya)

Kwando -

Tana nufin akwati ko mazubin da ake saƙawa, wanda ake amfani da shi wajen ɗaukar kaya ko adana abubuwa.

Misali; Ta je kasuwa da kwando don ɗaukar kayan miya.

ENG; Basket (A turance tana nufin kwando)

Kwangila -

Tana nufin yarjejeniya tsakanin ɓangarori biyu ko fiye domin gudanar da wani aiki ko ciniki.

Misali; Kamfanin ya samu kwangila domin gina sabon asibiti.

ENG; Contract (A turance tana nufin kwangila)

Kwangiri -

Tana nufin kwano mai faɗi da ake amfani da shi wajen ɗaukar yashi, siminti ko kaya a wurin aiki musamman aikin gini.

Misali; Magini ya ɗauki yashi a kwangiri zuwa saman bene.

ENG; Head pan for carrying sand (A turance tana nufin kwangiri)

Kwangwala -

Tana nufin doguwar sanda da ake amfani da ita wajen tuƙa jirgin ruwa ko kuma a matsayin sandar da ake rufi a gidajen gargajiya.

Misali; An sa kwangwala a kan rufin gidan Alaramma kafin a sa siminti.

ENG; Long pole used for canoeing or as roof pole of house (A turance tana nufin kwangwala)

1 208 209 210 211 212 337