Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Sweet made from ground tigernuts and groundnut - A turance tana nufin daƙuwa.
Misali; Zan kai wa amarya daƙuwa saboda idan ta yi baƙi ta ba su.
HAU; Daƙuwa (Tana nufin alawar da ake yin ta da niƙaƙƙiyar gyaɗa da aya da sikari)
Sweet pounded millet mixed with water - A turance tana nufin gumba.
Misali; An raba gumba a gidan mutuwar.
HAU; Gumba (Tana nufi dakakken garin gero da sikari da ruwa)
Swollen - A turance tana nufin hulu-hulu.
Misali; Idonsa ya yi hulu-hulu tun jiya saboda ciwo yake masa,.
HAU; Hulu-hulu (Tana nufin kumburi sosai)
Ta’adi - Ɓarnatarwa ko tozarta dukiya, kamar kwange ko coge ko wadaka da dukiyar kasa,ko samu da ɓarnar kuɗi ba bisa ka'ida ba.
Ta’ammali - Hulɗa ko kuma yin kowace irin mu'amala da wani abu kamar miyagun kwayoyi, kama daga kan yin kwayoyin da masu siyarwa zuwa kan masu sha.
Taekwondo Federation of Nigeria (TFN) - Hukumar Wasan Taƙwando Ta Najeriya
Take shelter or refuge - A turance tana nufin fake.
Misali; Lokacin da ruwan ya sakko a shagon na fake.
HAU; Fake (Tana nufin samun mafaka)
Taking good care of something - A turance tana nufin haba-haba.
Misali; Ana ta haba-haba da manyan baƙi.
HAU; Haba-haba (Tana nufin ba da kulawa ka'in da na'in)
Talata - Rana ce ta biyu a cikin ranakun mako.
Misali; Ana cin kasuwar duk ranar Talata.
ENG; Tuesday (A turance tana nufin rana ta biyu a mako)
Tall - A turance tana nufin dogo.
Misali;Na ga wani mutum dogo a ƙofar gida.
HAU; Dogo (Tana nufin mai tsayi)
Kishiyarta; Gajere