Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Jayayya - Tana nufin faɗi in faɗa. Misali; Tun safe suke jayayya a kan kuɗi. ENG; Controversy (A turance tana nufin jayayya)
Jaɓa - Tana nufin dabba mai kamar ɓera amma ta fi shi girma tana da dogon baki kuma tana wari. Misali; Akwai jaɓa a ɗakin nan don na ji warinta da na shigo. ENG; Stinking Shrew- Mouse (A turance tana nufin jaɓa)
Jealousy - A turance tana nufin kishi. Misali; Matan wannan zamani na da matuƙar kishi wanda ya saɓawa shari'a. HAU; Kishi (Tana nufin sosuwar zuciya da ɓacin ran da suke jawo fushi, a dalilin tarayyar da wani ya yi da wani, a kan abin da wanin ya keɓanta da son sa koma mallakarsa)
Jefi-jefi - Tana nufin ba kodayaushe ba. Misali; Yana zuwa gaishe da kakarsa jefi-jefi. ENG; Often (A turance tana nufin jefi-jefi) Kishiyarta; A kai-a kai
Jego - Tana nufin shayar da jariri. Misali; Indo jego take shi yasa ba za ta bi mu ba. ENG; Suckling of Infant (A turance tana nufin jego)
Jela - Tana nufin bindi. Misali; Jakin yana da doguwar jela. ENG; Tail (A turance tana nufin jela)
Jemage - Tana nufin dabba mai tashi sama wadda ba ta taɓa ƙasa. Misali; Akwai jemage a kan bishiyar ƙofar gida. ENG; Bat (A turance tana nufin jemage)
Jewa - Tana nufin je-ka-ka-dawo. Misali; Na gan shi yana ta jewa saboda tashin hankali. ENG; Going to and fro (A turance tana nufin jewa)
Jibga - Tana nufin ɗora kaya da yawa. Misali; Na ga Habu ya jibga kaya a jikinsa wai sanyi yake ji. ENG; Pile loads on top of one another (A turance tana nufin jibga)
Jibi - Tana nufin ranar da ke bin gobe. Misali; Jibi za a fara bikin kuma sai an jera sati ana yi. ENG; Day After Tomorrow (A turance tana nufin jibi)
1 176 177 178 179 180 337