Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Jiki - Tana nufin sassa gaba ɗaya daga kai zuwa ƙafa. Misali; Ya sha maganin ciwon jiki ya kwanta. ENG; Body (A turance tana nufin jiki)
Jima’i - Tana nufin saduwa tsakanin mace da namiji. Misali; Cututtukan sanyi na da nasaba da jima'i a lokuta da dama. ENG; Sexual Intercourse (A turance tana nufin jima'i)
Jimada Awwal - Tana nufin wata na biyar a watannin musulunci. Misali; A watan Jimada Awwal za a yaye ɗaliban. ENG; Fifth month of Islamic calendar (A turance tana nufin jimada awwal)
Jimilla - Tana nufin sakamako na bai ɗaya. Misali; Idan an haɗa kudina da naka za a samu jimillar dubu goma sha biyu. ENG; Sum Total (A turance tana nufin jimilla)
Jimina - Tana nufin nau'in tsutsuwa mai dogon wuya wadda ke yin ƙwai. Misali; Akwai jimina a gidan adana namun dajin da ke garinmu. ENG; Ostrich (A turance tana nufin jimina)
Jimiri - Tana nufin haƙuri da juriya. Misali; Duk wanda ya yi jimirin yin aiki zai samu kyakkyawan sakamako. ENG; Endurance/Patience (A turance tana nufin jimiri)
Jinga - Tana nufin yarjejeniyar biyan kuɗi. Misali; Mun yi jinga da shi zai biya ni da zarar na kammala aikin. ENG; Wages (A turance tana nufin jinga)
Jingim - Tana nufin adadi mai yawa. Misali; Ya tara kayan wanki jingim a ɗaki, da ƙyar zai iya wankewa shi kaɗai. ENG; Plentiful (A turance tana nufin jingim)
Jingina - Tana nufin bayar da ajiyar wata kadara domin rancen kuɗi da zimmar idan aka biya kuɗin sai a karɓa. Misali; Gidansa ya bayar jingina a banki ya karɓo bashin. ENG; Deposit given as a pledge for money borrowed (A turance tana nufin jingina)
Jini - Tana nufin sinadarin ruwa mai launin ja wanda zuciya take harbawa sassan jiki, yana ƙunshe da abubuwan da jiki ke buƙata domin rayuwa. Misali; Likita ya ce sai an ƙara masa jini leda ɗaya. ENG; Blood (A turance tana nufin jini)
1 178 179 180 181 182 337