Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Jiƙa - Tana nufin saka abu a cikin ruwa.
Misali; Ta jiƙa shinkafar tun safe saboda za ta yi wainar shinkafa.
ENG; Soak (A turance tana nufin jiƙa)
Joint Admission & Matriculation Board (JAMB) - Hukumar Jarabawar Shiga Jami'a
Joint Health Sector Union (JOHESU) - Kadaurar Ƙungiyoyin Malaman Lafiya
Joint Task Force (JTF) - Rundunar Hadin Guiwa
Judiciary Staff Union of Nigeria (JUSUN) - Ƙungiyar Jami'an ma'aikatar Shari'a Ta Najeriya
Jugum - Tana nufin zama shiru tare da saƙe-saƙe ko tunani.
Misali; Tun da na shigo ta yi jugum a zaune.
ENG; Despondently (A turance tana nufin jugum)
July - A turance yana nufin wata na bakwai a shekara.
Misali; A watan Yuli zai cika shekara biyar da gama makaranta.
HAU; Yuli (Wata ne na bakwai a shekara)
Juma’a - Rana ce ta biyar a ranakun mako.
Misali; Yara na ɗokin zuwa masallaci ranar Juma'a.
ENG; Friday (A turance tana nufin rana ta biyar a mako)
June - A turance wata ne na shida a shekara.
Misali; Damina na kankama a watan Yuni.
HAU; Yuni (Wata na shida a shekara)
Jure - Tana nufin dauriya.
Misali; Ta jure mugayen halayensa tsawon shekaru.
ENG; Endure (A turance tana nufin jure)