Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Kacal - Tana nufin kaɗai ko kaɗan.
Misali; Naira biyar kacal za ka biya ka ɗauki kayanka.
ENG; Mere (A turance tana nufin kacal)
Kaciya - Tana nufin cire fata daga jikin al'aurar namiji.
Misali; Yara shida aka yi wa kaciya a gidan.
ENG; Circumcision (A turance tana nufin kaciya)
Kaciɓis - Tana nufin haɗuwa ba zato ba tsammani.
Misali; Mun yi kaciɓis da Gwaggo a kasuwa ɗazu.
ENG; Meeting Suddenly (A turance tana nufin kaciɓis)
Kada - Tana nufin wata dabbamai kaushin baya kuma mai siffar ƙadangare da ke rayuwa a ruwa, amma tana da girma ainun.
Misali; Ruwan sama mai yawa ya sa kada ta fito daga gidan ajiyar namun daji.
ENG; Crocodile (A turance tana nufin kada)
Kadara - Tana nufin kaya masu daraja ko kayan kuɗi.
Misali; Sun buƙaci ya kawo takardun wata kadara kafin su ba shi rancen kuɗi.
ENG; Property (A turance tana nufin kadara)
Kadarko - Tana nufin ƙaramar gada da ake yi da katako musamman don kwararar ruwa.
Misali; A hanyar gidan maigari akwai kadarko.
ENG; Small Bridge (A turance tana nufin kadarko)
Kadaura - Babbar kungiya ko cibiya wadda ta hado mahimman bangarori masu zaman kansu ko kwararrun ma'aikata ko mutane.
Kaf - Tana nufi duka ko gaba ɗaya.
Misali; Ta kwashe kayanta kaf daga gidan, kun ga kenan ba ta niyyar dawowa.
ENG; Completely (A turance tana nufin kaf)
Kafa - Tana nufin ƙaramar hanya.
Misali; Ko yaya ɓeran ya samu kafa guduwa zai yi.
ENG; Small Hole (A turance tana nufin kafa)
Kafafen Intanet - Matattara ko inda ake samun bayanan da aka nema daga rumbon sadarwa.