Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Kafaɗa - Tana nufin sashen jiki da ke saman hannu. Misali; 'Yan mata na rawar girgiza kafaɗa a dandali. ENG; Shoulder (A turance tana nufin kafaɗa)
Kaffara - Tana nufin abin da mutum zai yi don karya rantsuwa ko sakamakon kisa da sauransu. Akan yi kaffara da azumi ko ciyarwa da sauransu. Misali; Azumi uku ake yi a kaffarar rantsuwa. ENG; Penalty to atone for breaking certain islamic law (A turance tana nufin kaffara)
Kafi - Tana nufin surkulle ko abin da ake sa wa a gida domin kariya daga ɓarayi ko rashin sa'a. Misali; Akwai kafi a saman soron gidan. ENG; Charm buried in front of door way or inside house for protection against misfortune (A turance tana nufin kafi)
Kafiri - Tana nufin wanda ba musulmi ba. Misali; Duk wanda ya yi sallah ba tare da alwala ba kafiri ne. ENG; Non-Muslim (A turance tana nufin kafiri)
Kaftani - Tana nufin taguwa mai faffaɗan hannu. Misali; Yayin kaftani ake yi yanzu. ENG; Caftan (A turance tana nufin kaftani)
Kai-dauki - Taimakawa ko kai agaji domin ceto.
Kaifi - Tana nufin ƙarfin da zai iya yanka. Misali; Wuƙar tana da kaifi sosai don ta yanke ni. ENG; Sharpness (A turance tana nufin kaifi)
Kaigama - Tana nufin ɗaya daga cikin sarautun gargajiya. Misali; An naɗa shi sarautar kaigama yau da safe. ENG; A traditional title (A turance tana nufin kaigama)
Kaji - Tana nufin jam'in kaza. Misali; An soya kaji za a yi mana miya da su. ENG; Chicken/Hen (A turance tana nufin kaji)
Kakabi - Tana nufin mamaki ko al'ajabi. Misali; Tun jiya muke ta kakabi saboda abin ya girmama. ENG; Suprise/Wonder (A turance tana nufin kakabi)
1 183 184 185 186 187 337