Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Jidali - Tana nufin rikici ko ɗawainiya.
Misali; Ya janyo wa kansa jidali tunda ya auri yarinyar nan.
ENG; Struggle/Trouble (A turance tana nufin jidali)
Jiddin - Tana nufin kodayaushe.
Misali; Ai Jiddin yana masallaci tunda Allah ya shirye shi.
ENG; Always (A turance tana nufin jiddin)
Jido - Tana nufin ɗebo kaya daga wani guri zuwa wani gurin.
Misali; Mun jido kayan daga tsohon gida zuwa sabo.
ENG; Removal of things to another location (A turance tana nufin jido)
Jigida - Tana nufin dutsinan ado da mata ke ɗaurawa a ƙugu.
Misali; Tana da jigida mai hawa goma.
ENG; Ornamental beads worn around hips by women (A turance tana nufin jigida)
Jigila - Tana nufin kai wa da komowa (kai-komo).
Misali; Kamfanonin jiragen sama na ta jigilar alhazai daga ƙasashe daban-daban.
ENG; Going back and forth (A turance tana nufin jigila)
Jiha - Tana nufin wani yanki daga cikin ƙasa.
Misali; An ƙirƙiri sabuwar jiha a ƙasar Najeriya.
ENG; State (A turance tana nufin jiha)
Jihadi - Tana nufin yaƙi don ɗaukaka addinin musulunci.
Misali; Sahabbai sun yi jihadi don ɗaukaka addinin musulunci.
ENG; Holy war to spread Islam (A turance tana nufin jihadi)
Jijiya - Tana nufin hanyar jini a jikin mutum ko dabba.
Misali; Allurar jijiya aka yi masa saboda zafin zazzaɓin.
ENG; Vein (A turance tana nufin jijiya)
Jijjiga - Tana nufin girgizawa.
Misali; Sai an jijjiga maganin sannan ake sha.
ENG; Shake (A turance tana nufin jijjiga)
Jika - Tana nufin yaro ko yarinyar da ɗa ko 'ya suka haifa.
Misali; Maƙoci na ya yi jika, jiya 'yarsa ta haihu.
ENG; Grandchild (A turance tana nufin jika)